
Daga UMAR GARBA a Katsina
Kananan hukumomin Malumfashi, Funtua da Bakori sun bi sahun wasu takwarorinsu da suka yi sulhu da ƴan bindiga a jihar da ke fama da matsalar tsaro.
Katsina na daga cikin jihohin Arewa maso Yammacin Nijeriya da ke fama da matsalar ƴan bindiga masu kai hare-hare a ƙauyuka da garuruwan jihar da kashe mutane da sace wasu domin neman kuɗin fansa.
An gudanar da zaman sulhun ne a garin Kakumi da ke yankin qaramar hukumar Bakori, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta bayyana.
Taron sulhun ya samu halartar shugabannin alumomin yankunan da wakilan ƴan bindigar.
A baya-bayan nan ana ta samun qaruwar qananan hukumomin Katsina da ke rungumar sulhu a wani mataki na magance matsalar tsaron jihar.
