Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ƙananan hukumomin Bakori, ƙanƙara ,Ƙafur, Funtua da malumfashi suka halarci zaman sulhun da ya gudana a garin Kakumi da ke ƙaramar hukumar Bakori.
A ɓangaren ‘yan bindigan akwai su Ado Aleru da Isiya kwashen Garwa da kuma Babano waɗanda sanannun ‘yan ta’adda ne da suka daɗe suna hallaka mutanen yankin.
Shugaban ƙaramar hukumar Bakori Alhaji Abubakar Musa Barde wanda ya ɗauki nauyin zaman ya bayyana zaman sulhun a matsayin babban al’amari da zai sake gina yarda da juna a tsakanin Hausawa da Fulani a yankin.
Shima ɗan majalisar dokoki da ke wakilan ƙaramar hukumar Bakori Hon.Abdulrahaman Ahmad Kandarawa ya ce wannan zaman sulhu babu wanda aka ba ko kobo a ɓangaren ‘yan bindigan.
Ya bayyana cewa yanzu alummar yankin da haɗin kan ‘yan bindigan za su yi ƙoƙarin maido da zaman lafiya da zumunta irin na yan’uwan taka a tsakanin su.
Tsohon babban jojin jihar kuma Galadiman Katsina.Hakimin Malumfashi Justice Sadiq Mahuta yayi kira da masu zaman sulhun da su tabbatar sun mutunta yarjejeniyar da aka cimma domin ɗorewar zaman lafiya a yankin da Jihar Katsina baki ɗaya.
Ado Aleru da yake magana a madadin ‘yan bindigan ya bayyana arangama da akai ta sami a tsakanin su da jami’an tsaro ya biyo bayan rashin yarda da juna a tsakanin su da yayi ƙamari.
Shi kuwa Indiya Kwashe wanda ɗaya daga cikin shugabannin ‘yan bindiga ne a yankin ya bayyana cewa mutanen su sun shiga harkar ta’addanci ne bisa rashin adalci da akai masu ” amma a yanzu a shirye muke mu ajiye makaman mu domin samun zaman lafiya a jihar Katsina baki ɗaya.
Malamai da dama sukai ta gudanar da addu’o’i na ɗorewar zaman lafiya a yankin.
Sai da yawa mutane na tambaya kan yadda ake gudanar da zaman sulhu da ‘yan bindiga ba tare da sun ajiye makaman su ba.
