Mutum 164,488 aka tabbatar sun kamu da korona a Nijeriya -NCDC

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Hukumar Yaƙi da Yaɗuwar Cututtuka ta Ƙasa (NCDC) ta bada sanarwar samun ƙarin mutum 65 da suka harbu da cutar korona cikin sa’o’i 24 a faɗin ƙasa.

NCDC ta ce ƙarin da aka samu ya shafi wasu jihohi su 11 ne ciki har da jihar Lagos-41, Kaduna-6, Kano-3, Rivers-3, Plateau-3 da kuma Akwa Ibom-2.

Sauran su ne; Imo-2 da Oyo-2 da Edo-1 da Bauchi-1 sai kuma jihar Osun mai mutum 1.

A cewar NCDC, jimillar mutanen da aka tabbatar sun harbu da annobar a faɗin ƙasa ya kama 164,488, yayin da mutum
154,441 sun warke, sannan mutum
2,061 sun rasu sakamakon cutar.

By Editor