Daga WAKILINMU
A sakamakon gargagaɗin da sashin kula da sha’anin abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya ya fitar ranar 29 ga Yuli game da yiwuwar fuskantar ƙarancin abinci a Arewacin Nijeriya, Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar ya ce ya zama wajibi gwamnati ta farga.
Gargaɗin na Majalisar Ɗinkin Duniya wani sabon tsari ne na kwarmata bayanai wanda ya kamata Gwamnatin Tarayya ta fuskanta kasancewar Arewacin ƙasar nan shi ne yankin da galibi ke samar da abinci da ake amfani da shi a faɗin ƙasa da ma wasu sassan Afirka.
Atiku ya ce halin ko-in-kula da gwamnati ke nunuwa game da barazanar yiwuwar samun ƙarancin abinci a fadin ƙasar nan abu ne mara daɗi da ka iya haifar da nadama.
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ya nunar cewa samun wadataccen abinci wani ɓangare ne na samar da tsaro, tare da cewa idan kuma aka gagara ɗaukar matakin magance hakan ba ka iya jefa Nijeriya cikin tarin matsaloli wanda zai iya shafar maƙwabtanta.
Daga nan, Atiku ya ba da wasu shawarwarin da a cewarsa muddin aka yi amfani da su, babu shakka za a samu mafita.
Shawarwarin sun haɗa da inganta tsaron ƙasa ta hanyar kafa hukumomin tsaron sa-kai na musamman da za su bai wa manoma kariya a gonaki, ɗaga wa manoma ƙafa game da basussukan da aka ba su, samar da ingantaccen irin shuki da dai sauransu.
