Rikicin ƙabilanci ya ci mutum huɗu a Filato

Aƙalla mutum huɗu ne aka tabbatar sun rasu tare da ƙona gidaje masu yawa sakamakon rikicin ƙabilancin da ya ɓarke a tsakanin Fulani makiyaya da matasan ƙabilar Irigwe a ƙauyukan ƙaramar hukumar Bassa a jihar Filato.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, ASP Ubah Gabriel, shi ne ya tabbatar da aukuwar rikicin, inda ya ce an ƙona gidaje kimanin hamsin a rikicin.

A cewar jami’in , “A ranar 31 ga Yuli 2021, ofishinsu ya samu rahoton aukuwar rikici tsakananin ‘yan bindiga da aka yi zargin Fulani ne da kuma matasa daga Irigwe a Jebbu Miango a ƙaramar hukumar Bassa ta jihar.

“Abin takaicin shi ne, an samu gidaje guda 50 da aka ƙona sannan an kashe wasu mutum huɗu.”

Ya ci gaba da cewa, faruwar lamarin ke da wuya suka tura jami’ansu zuwa yankin da rikicin ya faru don maido da zaman lafiya.

Ya ce Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, CP Edward Egbuka, tare da wasu manyan jami’an rundunar sun kai ziyarar gani da ido, kana ya ba da umarnin gudanar da bincike don gano musabbabin rikicin.

Bayanai sun nuna baya ga mutum huɗu da suka mutu yayin rikicin, wasu sama da mutum goma sun jikkata.