Allah Ya jiƙan Hajiya Umma Ali

Daga IBRAHIM MANDAWARI

A ranar Lahadin ta gabata, 01/08/2021, Hajiya Umma Ali ta amsa kiran Mahalicci, wato Allah ya karɓi ranta bayan gajeriyar rashin lafiya.
Babu shakka masana’antar shirya fina-finan Hausa da ma al’ummar musulmi bakiɗaya mun yi babban rashi wannan baiwar Allah.

Ta shigo wannan masana’anta tun wajajen shekarar 1998 kuma ta fara shirya fim tun a wannan lokaci da sunan Kamfaninta, wato UMMA ALI VENTURES. Haka kuma, sakamakon kyakkyawar mu’ala ya sanya kusan dukkan Jarumai a wancan lokaci suka mayar da gidanta tamkar gidajensu na haihuwa.

Hajiya Umma Ali ta raini maza da mata na wannan masana’anta ta hanyar riƙe su kamar ‘ya’yan da ta haifa tun suna ƙanana, daga cikinsu kuwa akwai babbar mawaƙiyar nan marigayiya Rabi Mustapha da su Ibrahim Sharu-Khan da su Dauda Kahutu Rarara da sauransu.

Wannan baiwar Allah ta na da halin karamci matuƙa, domin ta kan kashe kuɗi duk lokacin da za a yi taro domin girkawa da kawo abinci ga mahalarta taron, hasali ma har zuwa rasuwar nan tata, takan girko abinci kyauta ta kawo taron elders’ forum.

Umma Ali ‘yar asalin unguwar Yakasai ce cikin birnin Kano, kuma abokan karatunta a wannan masana’anta na primary school sun haɗa da su Marigayi Balarabe Sango.

Ta rasu ta bar mijinta wanda tsohon jami’in Hukumar Kula da Shige da Fice (Immigration) ne da ‘ya’ya (maza da mata) da jikoki ma su yawa.

Muna roƙon Allah ya ba ta Jannatil Firdausil a’ala, amin summa amin.