Sabon Shugaban Ƙasar Zambia, Hichilema ya caccaki tsohuwar gwamnatin Lungu

Spread the love


Sabon zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasar Zambia, Hakainde Hichilema, ya caccaki gwamnatin da ya gadana tare da bayyanata a matsayin gwamnatin danniya.

Hichilema ya caccaki tsohuwar gwamnatin ne a lokacin da yake yi wa ‘yan ƙasarsa jawabi a Litinin da ta gabata a matsayinsa na sabon zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasar. Tare da yi wa talakawansa alƙawarin samar musu da dimukuraɗiyya ingantacciya kuma mai tsabta.

Da yake jawabi jim kaɗan bayan da tsohon Shugaban Ƙasar, Edgar Lungu, ya amsa shan kaye, Hichilema ya ce shi da jama’arsa sun sha baƙar wahala a tsohuwar gwamnatin ƙasar.

Hichilema ya ce a matsayinsa na Shugaban Ƙasa, waɗanda suka zaɓe shi da ma waɗanda suka ƙi kaɗa masa ƙuri’a yayin zaɓen, kowa na shi ne.

A cewar rahotanni, sakamakon kusan ƙarshe ya nuna Hichilema ya samu ƙuri’u 2,810,757 yayin da abokin hamayyarsa Edgar Lungu yake da ƙuri’u 1,814,20.

Tuni dai Lungu ya amsa shan kaye a zaɓen inda ya taya Hichilema murnar zama Shugaban Kasar Zambia na bakwai.

Sa’ilin da yake jawabin bankwana ga ‘yan ƙasar Zambia, Lungu ya nuna godiyarsa dangane da damar da al’ummar ƙasar suka ba shi ta shugabancin ƙasar, yana mai cewa ba zai taɓa manta wannan karamcin da aka nuna masa ba.

By Editor