Daga ISAH BASHIR
A ranar Lahadin da ta gabata dubban mabiya Ɗariƙar Tijjaniya ƙarƙashin jagorancin Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi, suka gudanar da babban taron maulidi da suka saba shiryawa duk shekara karo na shida a garin Lafiya, babban birnin jihar Nasarawa.
Taron wanda aka gudanar a dandalin Lafia Squre, ya samu mahalarta daga ciki da wajen Nijeriya.
Gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi A. Sule, da Sarkin Lafiya, Mai Martaba Jastis Sidi Bage, da Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi da sauransu, na daga cikin waɗanda suka halarci taron.