’Yan bindiga sun sace sama da mutane 50 a Katsina

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Ɓarayin daji sun sace sama da mutum 50 a ƙauyen Ruwan Goɗiya da ke ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina.

Rahotanni sun tabbar da cewar maharan su fiye da 60 akan babura kimanin 30 sun kutsa kai a garin na Ruwan Goɗiya inda su ka yi ta yin harbi a kan mai uwa da wabi.

Wani mazaunin garin da aka sakaya sunansa ya shaida wa jaridar Daily trust cewa ‘yan bindigar sun ci karensu ba bu babbaka tsawon sa’a biyu, ba tare da wasu jami’an tsaro sun kai ɗauki ba, duk da cewa akwai sojoji kusan 20 a ƙauyen.

Mutumin ya qara da cewa, tun kafin ɓarayin su je garin mazauna garin sun samu bayani a kan shirin zuwan su kuma sun gaya wa jami’an tsaro, amma abin takaici maharan sun je da kusan ƙarfe 7:30 na al’muru, inda suka shafe sa’o’i biyu  su na ta’addanci.

‘’Sun raunata mutum uku amma ba su kashe kowa ba, sai dai kuma sun sace sama da mutum 50 bayan kwashe wasu kayayyaki da suka haɗa da tufafi,’’ inji mutumin.

Wani ɗan garin ya yi zargin cewa sojoji da suka fito daga ɓangaren garin Sheme na ƙaramar hukumar sun ga maharan suna tsallaka titi da mutanen da suka sace, amma kuma ba su yi wani yunƙuri na cetarsu ba.

Kafin wannan harin idan za a iya tunawa Manhaja ta kawo labarin yadda wasu ‘yan bindiga a ranar Lahadin makon jiya suka tada kasuwa da rana tsaka a ‘Yanɗaka ta ƙaramar hukumar Batsari inda su ka yi harbin kan mai uwa da wabi su ka kuma sace dukkan dabbobin da aka kawo kasuwar don sayarwa. 

Bayan nan ɓarayin sun tare hanyar Batsari zuwa Jibiya a ranar Lahadi inda suka buɗe wa wasu matafiya wuta a hanyar su ta zuwa cin kasuwa.

Haka zalika wata dabar ɓarayin daji akan babura ɗauke da muggan makamai sun yi dirar mikiya a garin Illela dake ƙaramar hukumar Safana inda su ka tarwatsa mazauna garin tare da yin awon gaba da dabbobi masu tarin yawa su ka kuma kashe kimanin mutane 12. 

Ƙananan hukumomin Batsari da Safana sun kasance cikin ƙananan hukumomi 13 da ke fama da hare-haren ɓarayin daji inda mazauna waɗannan ƙananan hukumomi ke bada labarin yadda ‘yan bindiga su ka addabe su duk da matakan da gwamnatocin jiha da na tarayya ke cewa su na ɗauka don shawo kan matsalar.

By Editor