Filayen gasar Olympics na lokacin sanyi za su ingiza cigaban wasannin ƙankara na Sin

Spread the love

Daga CRI HAUSA

A ranar 4 ga wata, an ƙaddamar da gasar Olympics ta lokacin sanyi da kuma taro karo na 5 na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta ƙasar Sin ta 13 a birnin Beijing, fadar mulkin ƙasar, wasu mambobin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta ƙasar waɗanda ke halartar taron sun bayyana cewa, Beijing ne birni na farko a faɗin duniya, wanda ya shirya gasar Olympics na lokacin zafi da na lokacin sanyi, don haka an gina wasu filayen wasa da ɗakunan wasa da dama a birnin, duk waɗannan za su taka rawa kan dauwamammen cigaban duniya.

A bayyane an lura cewa, birnin Beijing ya samu manyan sauye-sauye tsakanin shekarar 2008 zuwa 2022, haka kuma an samu saurin ci gaban ƙasar Sin cikin waɗannan shekarun da suka gabata, to game da yadda ake amfani da filayen wasannin Olympics bayan da aka kammala gasar?

Mamban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta ƙasar kuma mataimakin shugaban sashen tsara gine-gine na kwamitin shirya gasar Olympics na lokacin sanyi na birnin Beijing Shen Jin ya yi tsokaci cewa, gina filayen wasa bisa ma’aunin gasar Olympics, tare kuma da yin la’akari kan yadda za a sake yin amfani da su bayan kammala gasar, aiki ne mafi muhimmanci da sashen tsara gine-gine na kwamitin shirya gasar Olympics na lokacin sanyi na birnin Beijing ya yi, inda ya bayyana cewa, yayin da ake fasalin filayen wasa, an fi mai da hankali kan batun yadda za a gyara ko kuma sake yin amfani da su a nan gaba.

Fassarawa: Jamila daga CRI Hausa

By Editor