Mece ce kulawa a zaman aure? (2)

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Mai karatu sannu da jimirin bibiyar jaridar Blueprint Manhaja. Allah ya sa mu amfana da juna. Idan ba ku manta ba dai, mun faro da bayani kan ma’ana ta kulawa da kuma yadda take tasiri a zamantakewar aure. Da yardar mai dukka za mu ɗora daga inda mu ka tsaya.

Abin da na ke ƙoƙarin bayyana wa shine, mata har yau sun kasa bambance kulawa irin wannan ba lallai ta zama so na gaske ba, kuma ba sai wanda ya nuna irin wannan kulawa ne ke matuƙar son su ba. Wannan dalili yasa har yau an kasa shawo kan yawaitar matan da samari suka yaudara.

A ɓangare na biyu, akwai mutanen da ke nuna kulawa tsaka-tsaka. Ba ka cika gane soyayyarsu ta hanyar kulawa ba, har wani lokacin ka ji mata na ƙorafin mijina son da yake nuna mata hawa yake yana sauka, domin wani lokacin tamkar ba shi ba wurin nuna tarairiya da kulawa. Rashin maida hankali ke sa mace kasa gane hakan ne yanayin halittar mijin na ta, wani lokacin har ya yi sanadiyyar rigima tsakaninsu.

Ba za ku ƙiyawa zancena ba, idan kuka yi duba da yawan auren da ke samun matsala ta sanadiyyar rashin kulawa. Idan na ce kulawa a nan, ina nufin ta nuna soyayya ta hanyar kalamai masu daɗi, yawon shiririta tare da nuna muhinmancin matarka a baki.

Da yawa daga cikin matan da suke ƙorafin mazajensu basa masu kulawa irin wadda mijin wance ke mata, ko yadda muke gani a littafai ko finafinai, da za su ajiye hankalinsu, da sun fahimci irin yadda na su mazajen ke bayyana ta su kulawar, ya Allah lokacin da suke cikin damuwa, ciwo ko wani abu. Wanda wata kila ita waccan bata samu.

Akwai waɗanda sha kundum ne ta ɓangaren kulawa, waɗanda babu kulawa cikin tsarin halittarsu, ba wai hakan na nufin basa so ba, asalima a cikin waɗannan mutane an fi samun masu soyayar takalmin kaza. Sai dai iya bayyana son ne dai ba a hore masu ba. 

Ita kulawa ba kawai ta fatar baki ake bayyanar da ita ba kamar yadda mata da yawa suka ɗauka, ko ta hanyar nuna tarairiya da makamantanta ba. Kulawa kan iya zama wani hijabi da ke shiga tsakaninka da abin da ka iya cutar da kai ba tare da saninka ba.

Misali, mata da yawa da ke ƙorafin rashin samun kulawar mazajensu kan yi nadama ne a lokacin da suka samu kansu a wani ciwo ko wata lalura da ke buƙatar kulawa, a daidai lokacin da ta sa wa ranta mijinta zai guje ta, don ta jima dasa wa ranta ba ya sonta, sai kaga lokacin ne zai bata kulawa ta musamman, ya damu da damuwarta, sannan ya zame mata shinge da za ta jingina da shi.

Don haka nake kira ga mata masu ra’ayin haɗa so da kulawa su ba su ma’ana ɗaya, ku farka daga mafarkin da kuke yi, rayuwar fim da littafi wata duniya ce da ba taki ba, wadda aka yi don nishaɗi, sawa ranki maimaita ta a gidan aure na nufin kin sa kanki a hanyar da ba za ta fitar da ke kyakyawar hanya ba. 

Zaman aure ba yana nufin dole sai da kulawa irin ta nuna soyayya ba, ki ajiye hankalinki, ki fahimci irin na ki mijin kafin ki yanke hukunci kan zamantakewarki da shi. Zaman aure zai yiwu ko da ba irin wannan kulawa a ciki.

A ɓangaren iyaye, musamman mata, ku sanar da ‘ya’yanku mata ma’anar aure don kauce wa irin wannan fitina a zaman aure, domin sau da yawa ma’anar da muka ba wa auren ne ke tasirin a zaman auren. Yawan kallace-kallace kan ruɗa zukatan matasa har su shirya rayuwar aurensu da irin abin da suka kalla, hakan zai sa matsaloli su yawaita bayan auren.

By Editor