Babu wani ɗan Nijeriya da aka zalunta saboda addini, gwamnati ga Sanatocin Amurka

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A ranar Litinin ne Gwamnatin Tarayya ta yi Allah-wadai da kiran da wasu Sanatocin Amurka su biyar suka yi na neman a sake fasalin Nijeriya a matsayin ƙasar da ke nuna halin ko-in-kula kan cin zarafin addinai musamman ma Kiristoci.

Sanatocin da suka yi wannan kiran a wata wasiƙa da suka aike wa sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, sun kuma yi zargin tauye haƙƙin Kiristoci na gudanar da addininsu.

Da ya ke mayar da martani ga wannan zargi a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) a birnin Landan, Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya ce, kiran ya samo asali ne a kan ƙarya da kuma rashin fahimtar abubuwan da ke faruwa a ƙasar.

NAN ta ruwaito ministan ya tafi Landan ne domin ganawa da kafafen yaɗa labarai na duniya da kuma wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu.

“Idan za mu iya tunawa cewa, ‘yan watannin da suka gabata ne aka fitar da Nijeriya daga cikin jerin ƙasashen masu tauye ’yancin addini saboda an tabbatar da cewa babu wata hujja a kan zargin cewa ana tsananta wa Kiristoci ko wani addini ko kuma an hana mutane gudanar da ayyukansu na addinin da suka zaɓa.

“Muna so mu sake cewa Nijeriya ba ta da wata manufa da za ta hana mutane ’yancin yin addininsu. Haka nan ƙasar ba ta da wata manufar tauye ’yancin yin addini, kuma ba gaskiya ba ne Nijeriya na tsananta wa kowa saboda ra’ayinsa,” inji shi.

Mohammed ya bayyana cewa, kundin tsarin mulkin Nijeriya ya ba wa kowa ’yancin yin addininsa ba tare da cin zarafi ba, kuma gwamnati na kiyaye tanadin tsarin mulki da kishi.

Ya ƙara da cewa, yawancin masu sharhi da ba su da masaniya kan harkokin siyasa da abubuwan da ke faruwa a Nijeriya sun ɗauki laifuka da faɗace-faɗacen ƙabilanci a matsayin batutuwan da suka shafi addini.

“Babu wani mutum a Nijeriya da ake zalunta, amma muna da batutuwan da suka shafi aikata laifuka, kuma masu laifi ba sa banbance kowane addini.

“Suna yin garkuwa da mutane don kuɗi, suna riƙe mutane a kan kuɗin fansa ba tare da la’akari da addininsu ba.

“Idan ana son a yi ƙididdiga, zan iya faɗa da kwarin gwiwar cewa, Musulmai da yawa kamar Kiristoci sun sha fama da waɗannan masu laifi,” in ji shi.

Ministan ya ci gaba da cewa, lungiya ɗaya tilo da aka sani da ke kai wa Kiristoci hari ita ce ISWAP.

Sai dai ya ce, gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da manyan ayyukan soji domin kakka:e masu laifin, kuma tana samun sakamako mai kyau.

Ministan ya ce, wasu lungiyoyi masu zaman kansu kuma suna ciyar da ƙasashen duniya bayanan da basu dace ba domin samun kuɗaɗe daga masu hannu da shuni.

Mohammed ya sake nanata cewa, manyan addinan biyu a Nijeriya – Musulunci da Kiristanci – su ma suna hafa kai don ganin an warware rikicin da kuma mayar da ƙasar kan turbar zaman lafiya.

Ya ba da misali da Ƙungiyar Haɗin Kan Addinai ta Nijeriya (NIREC) da ke ƙoƙarin samar da haɗin kai da fahimtar juna a tsakanin addinan Kirista da na Musulunci.

Ministan ya nemi tallafi daga ƙungiyoyi da dama da kuma ƙasashen waje wajen tunkarar ƙalubalen matsalar tsaro a Nijeriya.

By Editor