Babu jarrabawa a ranar Babbar Sallah, inji NECO

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Jarrabawa ta Ƙasa, NECO ta ce ba za a yi jarrabawa a ranar 9 ga watan Yuli ba, savanin raɗe-raɗin da wasu ke yi na cewa za a yi jarrabawa a ranar Eid-el-Kabir.

Majalisar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da babban jami’in yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Azeez Sani, ya raba wa manema labarai a Abuja ranar Litinin.

Ya ce hukumar tana sane da muhimmancin bukukuwan addini, don haka a ko da yaushe ta kan yi tsari da tanadin irin waɗannan ranakun wajen sanya ranar jarrabawa.

“Hukumar ta ayyana mako guda ba jarrabawa, wanda ya fara daga ranar 8 ga watan Yuli zuwa 13 ga watan Yuli, a jarrabawar kammala makarantun sakandare (SSCE) da ke gudana ɗaliban da ke makarantu.

“An yi haka ne don bai wa Musulmai masu aminci damar samun isasshen lokaci yin bikin,” inji shi.

Idan dai ba a manta ba a ranar 27 ga watan Yuni ne aka fara gudanar da jarrabawar kammala makarantun sakandare ta shekarar 2022, SSCE, wadda za a kammala a ranar 12 ga watan Agusta.

By Editor