HOTUNA: Kirista sun taya Musulmi gyaran Masallacin Idi a Kaduna

Yayin da al’ummar Musulmi ke shirye-shiryen bikin Babbar Sallah, wasu matsa da dattawan Kirista a yankin Ƙaramar Hukumar Kachia a Jihar Kaduna, sun haɗa kai wajen taya musulmin yankin gyaran filin Masallacin Idi a ƙarshen makon da ya gabata.

Bayan da aka yaɗa hotunan a soshiyal midiya, masu amfani da kafafen sun tofa albarkacin bakinsu, inda galibi suka yaba da hakan tare da nuna irin wannan shi zai taimaka wajen inganta haɗin kan ƙasa da kuma zaman lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *