Daga UMAR GARBA a Katsina
Masarautar Jihar Katsina wadda mai Martabata Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumin Kabir Usman ke jagoranta, ta sanar da cewa ba za ta gudanar da hawan Sallah ba kamar yadda aka saba a bana.
Bayanin hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da masarautar ta fitar wa manema labarai a cikin wata takarda mai ɗauke da sa hannun mai taimaka wa sakataren masarautar kuma wato Sarkin tsaftar Katsina Alhaji Sule Mamman Dee.
Sai dai sanarawa ta bayyana cewar mai martaba sarki zai halarci Sallar Idi idan Allah ya kaimu ranar Asabar da ake sa ran gudanar da Sallah a duk faɗin ƙasar nan.
Daga nan sai masarautar ta umarci al’umma da su yi amfani da ranar sallar don yi wa jihar Katsina dama ƙasar nan baki ɗaya addu’o’in samun dawwamammen zaman lafiya.
Kafin zuwan wannan sanarwa a ƙarshen makon da ya gabata ne masarautar ta sanar da al’ummar jihar cewar sarki zai yi hawan Sallah, amma hawan Sallah kaɗai banda na bariki lamarin da ya saka al’ummar jihar cikin farin ciki duba da yadda yara da mata har ma da manya ke son ganin sun saka sababbin tufafi sun fita kallon sallar, wanda masarautar jihar ke gudanarwa a lokacin bukukuwan ƙaramar Sallah ko babba, inda sarkin kan yi hawa har sau biyu wato ranar da aka gudanar da Sallar Idi da kuma washegarin Idi wanda aka fi sani da hawan bariki.
