Daga CMG HAUSA
Yau ne, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya aike da wasiƙar taya murna ga taron dandalin tattaunawa kan zaman lafiya da tsaro na ƙasar Sin karo na biyu.
Xi ya jaddada cewa, ƙasashen Sin da Afirka abokai ne na kwarai, kuma abokan hulɗa, kana ‘yan uwa na ƙwarai, waɗanda ke tsayawa tsayin daka a kowane irin hali suna kuma taimakon juna.
A halin yanzu, duniya tana fuskantar manyan sauye-sauyen da ba a taba gani ba a cikin ƙarni cikin sauri.
Kuma har yanzu annobar COVID-19 tana yaɗuwa, kuma ƙalubalen tsaro daban-daban na ci gaba da bayyana, inda suke haifar da ƙalubalen da ba a taba ganin irinsa ba ga ɗaukacin dan Adam.
Xi ya ce, tabbatar da zaman lafiya da tsaro mai ɗorewa a duniya, shi ne burin jama’ar Sin da Afirka na bai daya. Har kullum ƙasar Sin tana kiyaye tsarin haɗin gwiwa da fahimtar juna na zahiri, da son yin hadin gwiwa tare da ƙawayen Afirka, da dagewa kan haɗa kai, da hadin gwiwa, da tabbatar da tsaro mai dorewa, da kiyaye MƊD a matsayin tushen tsarin ƙasa da ƙasa, da kiyaye adalci a duniya, da yayata aiwatar da shirin tsaro na duniya, da gina kyakkyawar makomar al’ummar Sin da Afirka na sabon zamani.
An gudanar da taron dandalin tattaunawar zaman lafiya da tsaro na ƙasar Sin da Afirka karo na biyu, ta kafar bidiyo, bisa taken “Ƙarfafa hadin gwiwa don samar da tsaro cikin haɗin gwiwa”.
Fassarawar Ibrahim
