Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Makarantar ST Lous mai tsohon tarihi da ke Unguwar Bamfai a birnin Kano, ta yi bikin walimar taya ɗalibanta 29 murna da suka samu falalar rabauta da sauke karatun Alƙur’ani maigirma, a walimar da hukumar makarantar ta shirya musu wadda aka yi a harabar makarantar a ranar Larabar da ta gabata, kamar yadda Malama Halima Baba Yaro, mataimakiyar shugabar makarantar kuma wacce ta jagoranci bikin walimar ɗaliban 29, ta bayyana a lokacin walimar.
Har ila yau, Malama Halima Baba Yaro, ta ce wannan ranar ba ƙaramar rana ba ce ga hukumar makarantar da malamai, da iyayen yara da su kansu ɗalibai da suka yi sauka, da ma wanda ba su yi ba, da sauran al’ummar Musulmi na makarantar da wajen ta kasancewar Alƙur’ani maigirma na a matsayin babban littafi ga ɗaukacin al’ummar Musulmi na duniya.
A ƙarshe ta bayyana cewa karatun da ake yi a ranar Asabar da Lahadi ana yi ne da ɗaliban da suke cikin makarantar da kuma ɗaliban makarantar amma ba a ciki suke ba, su na shigowa ne su yi karatu a ranakun hutu kuma wannan ya samo asali ne daga ƙoƙarin malaman masu koyarwa ba gajiyawa, don haka ne ta yaba musu kan ƙoƙarin su da kishinsu na ba ɗaliban Ilimi, da tarbiyya, bisa goyon baya da taimakon na ƙungiyar iyaye da malaman makaranta na ST.Lous kamar irin su Hon. Alhassan Zainawa da ɗaukacin shugabannin ƙungiyar da mambobinsu.
