Ginin bene ya rufta a Kano

Spread the love

Wani ginin bene da ke hanyar Beirut daura da hanyar Ibrahim Taiwo a birni Kano, ya rufta.

Wani mai amfani da shafin Tiwita, Devdeiz, ya wallafa a shafinsa ranar Talata cewa, ginin da ya rufta ɗin ana kan aikin gina shi ne.

Ya zuwa haɗa wannan rahoton babu wani ƙarin bayani a hukumance dangane da iftila’in.

Wannan na zuwa ne ƙasa da mako ɗaya da ruftawar wani gini a yankin Kubwa a Abuja.

A ‘yan lokutan baya-bayan an fuskanci ruftawar gine-gine a sassan Nijeriya, musamman a Jihar Legas, lamarin da masana ke danganta shi da rashin amfani da kayan gini masu inganci.

By Editor