Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin ƙarin harajin kiran wayar sadarwa da ofishin kasafin kuɗi na Nijeriya ke ƙoƙarin yi.
Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki a Fasahar Zamani, Isa Ali Pantami ne ya sanar da dakatarwar a ranar Litinin yayin taron ƙaddamar da Kwamitin Shugaban Ƙasa na haraji kan hanyoyin sadarwa don bunƙasa ɓangaren tattalin arziki ta hanyar fasahar zamani a Abuja.
Ministan ya ce tun tuni fannin sadarwa ya cika da harajai da yawa.
Gwamnatin Tarayya ta hannun ofishin kasafin kuɗi na tarayya a baya ta bayyana cewa za ta fara aiwatar da shirin fitar da kuɗaɗen da ta ke buƙata a kan harkokin sadarwa da abubuwan sha a shekarar 2023.
Sai dai Pantami ya ci gaba da cewa ba ya goyon bayan aiwatar da wannan harajin da zai ƙara tsadar harkokin sadarwa ga ‘yan Nijeriya.
