Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Rahotanni daga Jihar Kogi na cewa ‘yan fashi da makamai sun far wa rassan bankunan Zenith, da UBA da First Bank da ke ƙaramar hukumar Ankpa.
BBC ta rawaito cewa lamarin ya faru da tsakar rana, inda ɓarayin suka yi awon-gaba da maƙudan kuɗaɗen da ba a san adadinsu ba.
Ganau sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa, ‘yan fashin sun zo bankunan cikin ƙananan motoci da babura da bas-bas, inda suka wawushe kuɗin da ke bankunan da wurin hada-hadar kasuwancin kuɗi na POS da ke kusa da bankunan.
‘Yan bindigan sun yi ta harbi kan mai uwa da wabi kafin su tsere ba tare da kama ko guda ɗaya daga cikinsu ba, sun kuma shafe sa’o’i su na gudanar da aikin.
Wani mazaunin kusa da inda lamarin ya faru, ya shaida wa Daily Trust cewa mutane sun shiga gida lokacin da suka fara harbin kan mai tsautsayi.
Kuma jami’an tsaro ba su isa wajen ba har sai bayan sun gama cin karensu ba babbaka.
