Muna ɗaukar mata aiki amma sai wacce ta dace – Kwamandan vijilante na Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Kwamandan ƙungiyar tsaro ta vijilante a Jihar Kano, Shehu Rabi’u ya ce suna ɗaukar mata aiki, domin akwai rawar da suke takawa a wajen tsaron jihar.

Da ya ke zantawa da manema labarai a ofishinsa a Kano ranar Talata, Rabi’u ya ce ba ko wacce irin mace su ke ɗauka aikin tsaro ba, sai wacce ta dace.

Ya ce suna ɗaukar ma’aikata aiki waɗanda shekarunsu suka fara daga 18 zuwa 40, inda ya qara da cewa su na yin duba na tsanaki kafin ɗaukar ma’aikata domin guje wa ɗaukar bara-gurbi cikin al’umma.

“Mukan ɗauki mata aiki na vijilante sabo da suma akwai rawar da suke takawa wajen magance ayyukan ɓata-gari, amma fa mu na ɗaukar mata ne da yardar iyayensu ko mijinsu ko wani shaƙiƙi nasu, don gudun yin kitso da ƙwarƙwata,” inji Shehu Rabi’u.

Ya ce zuwa yanzu an samu ci gaba mai tarin yawa a faɗin jihar Kano ta fuskar tsaro, kuma hakan na da alaƙa da irin yadda jami’an ƙungiyar vijilante ke gudanar da aikinsu ba dare ba rana domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

”Duk lokacin da kake tafiya cikin dare za ka ga jami’an suna zagayawa cikin unguwanni a tsakiyar dare, wannan ya ƙara taimakawa wajen inganta tsaro, inda harkokin ƙwacen waya suka taƙaita sosai a jihar Kano,” inji Kwamandan.

Ya ce akwai kyakyawar alaƙar aiki tsakaninsu da sauran hukumomin tsaro dake Kano, musamman ‘yan sanda, saboda su suke kaiwa masu laifi idan sun kama don yin bincike tare da turasu kotu domin girbar abinda suka shuka.