Sin ta yanke shawarar sanya takunkumai a kan shugabannin kamfanonin Amurka da ke da hannun sayar da makamai ga Taiwan

Spread the love

Daga CMG HAUSA

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Mao Ning, ta shaida wa taron manema labaru da aka saba yi Jumma’ar nan cewa, domin kare martabar ƙasar Sin da moriyar tsaron ƙasar, gwamnatin ƙasar Sin ta yanke shawarar ƙaƙaba takunkumai kan jagororin kamfanonin Raytheon Technologies da Boeing Defense na ƙasar, saboda hannun da suke da shi a makaman da Amurka ta sayarwa yankin Taiwan na ƙasar Sin.

Bayan da Amurka ta sanar da shirinta na sayar da makaman da darajarusu ta dalar Amurka biliyan 1.106 ga yankin Taiwan a ranar 2 ga watan Satumba, ƙasar Sin ta bayyana cewa, za ta ɗauki ƙwararan matakai masu ƙarfi don tabbatar da kare ‘yancin kai da muradunta na tsaro.

Mai fassarawa: Ibrahim

By Editor