Nijeriya ta fara raba kayayyakin kiwon lafiya ta hanyar jirgi mara matuƙi

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Nijeriya ta kafa tarihi sakamakon bin sahun wa su ƙasashen duniya kamar Ghana da Rwanda da a cikin sauƙi suke rarraba kayayyakin kiwon lafiya, waɗanda suka haɗa da magunguna da jakakkunan jini ga wuraren da suke da wuyar ratsawa da jirage marasa matuƙa.

Haka maganar take kamar yadda jirgi maras matuƙi mai gudanar da hidimomi na kamfanin, Zipline, ya fara rarraba kayayyakin kiwon lafiya ba tare da matuƙi ba wa cibiyoyin kiwon lafiya dake cikin Jihar Kaduna.

Kamfanin ya bayyana cewar, kayayyakin kiwon lafiya, da ma wasu kayayyakin lodin farko da aka aza wa jirgin an samu nasarar isar su cibiyar kiwon lafiya na garin Galadimawa dake cikin qaramar hukumar Kauru ta jihar Kaduna.

Cibiyar kiwon lafiya ta Galadimawa tana ɗaya daga cikin cibiyoyin kiwon lafiya da aka ayyana jirgin zai raba kayayyakin da aka umurci jirgin na Zipline da kai wa cikin tafiyar gaggawa da aka yi nufinsa da shi.

Pambegua ita ce cibiyar ɗaukar kayayyakin rabawar wa cibiyoyin kiwon lafiya a Jihar Kaduna, kuma ita ce cibiyar ta farko da jirgi maras matuqi ya fara aiki da ita a ɗaukacin faɗin ƙasar Nijeriya, da yake taimaka wa gwamnati wajen rabon ire-iren waɗannan kayayyaki a jihar.

Da yake yin jawabi jim kaɗan bayan da jirgi maras matuƙi ya rarraba kayayyakin, wani ma’aikacin kiwon lafiya a cibiyar ta Galadimawa, Chongfilawos Irimiya, ya ce, “mun gode wa Allah da samun Zipline. Muna cikin daji na rashin sadarwa tsakaninmu da manyan cibiyoyin kiwon lafiya dake birane. Mukan yi tafiya mai nisa kafin mu cimma waɗancan manyan cibiyoyi domin samun kayayyakin kiwon lafiya zuwa namu cibiyoyin, lamarin da ya kasance mawuyaci, amma da taimakon Zipline, duk waɗannan batutuwa sun kasance tarihi.”

Ita ma da yake tofa albarkacin bakinsa, Manajar kamfanin na ‘Zipline Nigeria’, Ms. Catherine Odiase, ta ce tun lokacin da aka ƙaddamar da Zipline a watan Yuni, 2022, tana mu’amala da hukumar tuƙi a sama domin samun amincewar yin safara a sararin samaniyyar Jihar Kaduna.

Odiase ta yaba wa waɗancan hukumomi da suka baiwa Zipline damarmakin yin safara, ta ƙara da cewar, “kamfanin yana matuƙar samun wannan amincewar a yi wa sashin kiwon lafiya tagomashi,” ta ƙara da cewar, ‘kimiyyarmu ta nuna cewar jigo ce ta taimaka wa gwamnati cimma nasarori a fannin kiwon lafiya.

“Bisa wannan tsari, za mu sadaukar da kanmu wajen taimaka wa gwamnatin jihar Kaduna domin cimma nasarorin wannan manufa na rarraba kayayyakin kiwon lafiya zuwa ga al’ummomi a dukkan sassan jihar cikin mintuna 40 na lokaci, ko ma ƙasa da haka.

Ta sha alwashin Zipline zai cigaba da haɗa kai da gwamnatoci domin tabbatar da cewar, babu wani mahaluƙi da aka yi tasgaro a fannin kiwon lafiya a dukkan sassan ƙasar nan.

Cibiyoyi uku na farko na ɗaukar kayayyakin kiwon lafiya domin rabawa da za a zayyana a cikin jihar Kaduna suna da kuzarin raba kayayyaki wa cibiyoyin kiwon lafiya guda 500 a da’irar kilomita 80 da gaggawar tafita ta kilomita 110 cikin sa’a guda, walau dare ko rana, ruwan sama ko bazara.

“A watan Fabrairu ne na shekarar 2021, Zipline ya ayyana aniyarsa ta zayyana cibiyoyin rabo guda uku a Jihar Kaduna, da taimakon Gwamnatin Tarayya, domin samun hidimomin Zipline”.

Nijeriya ita ce qasa ta uku a nahiyar Afurka da suka fara cin gajiyar hidimomin Zipline, bayan ƙasashen Ghana da Rwanda, kana Kenya da Cote d’Ivoire za su ƙaddamar da wannan shiri a ƙarshen wannan shekara da muke ciki.