Ambaliyar ruwa ta rushe gidaje sama da 200 a Zariya

Spread the love

Daga MOH’D BELO HABIB a Zariya

Ambaliyar ruwa ya rushe gidaje sama da 200 a cikin garin Zariya dake ƙaramar hukumar Zariyan cikin jihar Kaduna.

Wakilin Manhaja wanda ya zaga yankunan da abin ya shafa, ya ruwaito cewa gidajen da al’amari ya shafa galibansu gidajen talakawa nw kuma ambaliyar ruwan na da nasaba ne da ruwan da aka dinga sheƙawa yi akai akai har na tsawon kwanaki huɗu ko biyar a jere.

Binciken da wakilin Manhajar ya gudunar a unguwannin da iftila’in ya shafa kamar Kusfa, Unguwar Malam Sule, Unguwar Danjinjiri, Kan Fage, Rimin Doko, Unguwar Nufawa da dai sauransu, ya bayyana cewa gidajen ginin ƙasa ne kuma waɗanda abin ya shafa talakawa ne masu neman na yau da gobe ba masu ƙarfi ba.

Da yake zantawa da wakilinmu Malam Abubakar Sadiq Aliyu Mai Unguwar Kusfa ya koka akan wannan iftila’in ya ce waɗanda da matsalar ya shafa basu da ƙarfin gyara muhallin nasu saboda matsin tattalin arziki.

Malam Aliyu ya danganta ambiliyar ruwa da rashin isassaun magudanar ruwa a cikin birnin na Zariya kashi kududdufan dake tare ruwa antoshesu anyi gine-gine.

Mai unguwan ya yi kira ga hukumar again gaggawa ta jihar Kaduna wato SEMA da ta kawo ma waɗanda abin ya shafa gudunmuwa kasancewarsu talakawa ne.

Malam ya yaba da ƙoƙarin da ƙaramar hukumar Zariya na giggina magudanar ruwa a dukkan gundumomin dake cikin birnin Zariya, sai kuma ya yi kiran ƙaramar hukumar da ƙara giggina magunar ruwa domin kaucewa ambaliyar nan gaba.

By Editor