Sarkin Kano ne uban gidauniyar ELS ta taimaka wa marayu – Adosuwa Ogechi

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Shugabar gidauniyar tallafa wa iyayen marayu, mata, da sauran masu rauni mabuƙata da ake kira ELS Empowerment Foundation, Misis Adosuwa Ogechi Udo, ta bayyana Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero a matsayin uban gidauniyar, saboda kasancewarsa mutum mai tausayin marayu da gajiyayyu.

Ohechi ta ce babban aikin gidauniyar tasu shi ne koyar da mata iyayen marayu da makamantansu sana’o’in da su ka shafi girke-girke, ɗinke-ɗinke saƙa da sauran sana’o’i na dogaro da kai, musamman ga mata waɗanda mazajensu suka rasu ko kuma waɗanda suka rabu da mazajen su sakamakon matsaloli na rayuwa da ƙaddara take kawo wa kuma wannan dalili ne ya sa yanzu haka wannan gidauniya ta ELS Empowerment Foundation ta zo Kano don tallafawa ga raunana kamar yadda ya kasance shi ne maƙasudin kafa gidauniyar.

A cewar shugabar gidauniyar, ganin kyakyawar manufar gidauniyar ya sa mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya kasance uban gidauniyar mai taimakawa marayu a Nijeriya.

Madam Adosuwa Ogechi Udo, ta bayyana haka ne a lokacin da take zantawa da manema labarai a lokacin buɗe bitar kwana bakwai da ta shirya wa mata iyayen marayu da zawarawa da sauran mabuqata mata sama da 80 bitar koyar da sana’o’i da girke-girken abinci zamani da na gargajiya a gidan ajiye kayayyakin tarihi na Makama da ke Kano a ranar Litinin da ta gabata.

Ogechi ta yi kira da shugabanni na kowanne mataki da ‘yan siyasa da sauran shugabannin al’umma kan su riƙa taimakawa irin waɗannan bayin Allah ta hanyar ɗaukar nauyin koya musu sana’o’i da kuma basu jari domin tallafar kansu da ‘ya’yan su a fannin ilimi da sauran al’amuran yau da kullum, inda kuma ta yaba wa mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, da sauran masu taimakawa marayu a Kano da ma duk inda suke a duniya.

A ƙarshe Hauwa’u Umar Kankarofi, ɗaliba ce da ta kammala karatu a makarantar koyar aikin lafiya ta ce sana’o’i iri-iri da ake koyarwa a wannan gidauniya ta ELS Empowerment Foundation, da kuma damar da ta samu na shiga wannan bita ya sa ta zamo ɗaya daga cikin waɗanda su ke koyon wannan sana’a a wannan lokaci, inda Malama Fatima Usman Goron Dutse, ɗaya daga cikin iyayen marayu da suka halarci wannan bita ta bayyana farin cikinta da jin daɗi da samun damar zuwa koyon sana’o’i na ELS Empowerment Foundation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *