Daga CMG HAUSA
A yau ne, ƙasar Sin ta watsa darasi na farko game da kimiyya da aka shirya daga ɗakin gwaje-gwaje na Wentian na tashar binciken sararin samaniyar ƙasar Sin.
Wannan shi ne aji na farko da ‘yan sama jannatin kumbon Shenzhou-14 wato Chen Dong da Liu Yang da Cai Xuzhe suka gabatar, waɗanda aka harba su zuwa tashar binciken sararin samaniyar ƙasar a ranar 5 ga watan Yuni, don gudanar da aiki na tsawon watanni 6, kuma irinsa na 3 da ‘yan sama jannatin na ƙasar Sin suka gabatar daga sararin samaniya.
Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa
