Daga CMG HAUSA
Mai magana da yawun babban taron wakilan JKS Sun Yeli, ya bayyana cewa, yau Lahadi 16 ga wata ne, za a buɗe babban taron wakilan JKS karo na 20 da misalin ƙarfe 10 na safe, a babban ɗakin taron jama’a dake birnin Beijing, fadar mulkin ƙasar Sin, za kuma a kammala taron a ranar 22 ga watan Oktoba, inda za a shafe kwanaki 7ana gudanar da shi
Bugu da kari Sun ya bayyana cewa, an tabbatar da cancantar wakilai dubu 2 da 296 waɗanda za su halarci babban taron wakilan JKS karo na 20.
Inda za su wakilci mambobin JKS sama da miliyan 96 da kuma sama da miliyan 4.9 a matakin farko na ƙungiyoyin jam’iyyu.
An tattara ra’ayoyin jama’a sama da 4,700 game da daftarin rahoton kwamitin koli na JKS na 19 da aka gabatarwa babban taron wakilan JKS karo na 20.
Wakilan sabon zaunannen kwamitin ofishin siyasa na kwamitin ƙoli na JKS karo na 20, za su gana da manema labarai na ƙasar Sin da na ƙasashen ƙetare bayan kammala cikakken zama na farko na kwamitin ƙolin JKS na 20.
Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa
