Daga CMG HAUSA
A yau Litinin ne mataimakin darektan ofishin kula da kwaskwarima na kwamitin ƙolin jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin, kuma mataimakin darektan hukumar kula da kwaskwarima da raya ƙasa ta ƙasar Mu Hong ya bayyana cewa, rahoton babban taron wakilan JKS karo na 20, ya mayar da samun ci gaba mai inganci a matsayin babban aiki na zamanantar da ƙasa mai bin salon gurguza daga duk fannoni, lamarin da ya sake shaida cewa, ingancin samun ci gaba yana da ma’ana matuƙa.
Mu Hong ya faɗi hakan ne a yayin taron ganawa da manema labarai da aka shirya, domin ƙara fahimtar rahoton babban taron wakilan JKS karo na 20, inda ya yi nuni da cewa, rahoton ya tsara manufofi a ɓangarori shida bisa manyan tsare-tsare kan batun, game da yadda za a ingiza ci gaba mai inganci, waɗanda ke haɗa hanzarta aikin tsara ayyukan raya ƙasa, da tabbatar da manufar raya ƙasa ta hanyar yin ƙirƙire-ƙirƙire, da kafa tsarin tattalin arzikin kasuwar tsarin gurguza mai inganci, da farfado da ƙauyuka daga duk fannoni a fadin ƙasar, da ciyar da yankunan ƙasa gaba yadda ya kamata, da ƙara buɗe ƙofa ga ƙetare.
Jami’in ya ƙara da cewa, manufofin za su ƙara imanin al’ummomin ƙasa da ƙasa kan ci gaban ƙasar Sin.
Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa
