Daga CMG HAUSA
A yau Litinin ne darektan ofishin nazarin manufofin raya ƙasa na kwamitin ƙolin JKS Jiang Jinquan, ya bayyana a yayin taron ganawa da manema labarai da aka shirya, domin ƙara fahimtar rahoton babban taron wakilan JKS karo na 20 cewa, cimma burin tabbatar da wadata a faɗin ƙasa, aiki ne da ake yi cikin dogon lokaci, kuma ya dace a gudanar da shi bisa matakai daban daban.
Jami’in ya kara da cewa, dalilin haka shi ne, haƙiƙanin yanayin da ƙasar Sin ke ciki, wato har yanzu ƙasar Sin ƙasa ce mai tasowa, kamata ya yi a rika tattara dukiyoyin zamantakewar al’ummun ƙasar, domin daga matsayin rayuwar al’ummun ƙasar, kuma ya dace a yi kokari bisa matakai daban daban, ta yadda al’ummun ƙasar za su ga sauyi daga sakamakon da aka samu.
Mai fassarawa: Jamila daga CMG Huasa
