Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Sabuwar na’urar da hukumar zaɓen Nijeriya ta kawo don zaɓen 2023 wacce an fara ma aiki da ita mai taken BVAS, a taƙaice ta zama bun ambatawa a duk lokacin hukumar ta zaɓe ko wani jami’i da sauran masu ruwa da tsaki za su yi magana da ke nuna ɗaukar matakan hana maguɗi.
Zave a Nijeriya kan zama wanda ya samu nasara ko da gaskiya ko kuwa a’a ya yi ta murna hakanan wanda bai samu nasara ba ta hanyar gaskiya ko murɗiyar maguɗi ka ga ya na ƙorafi da tafiya kotu.
Ba a faye samun wanda ya faɗi zace ya amince kai tsaye da kaye ba ba tare da kure duk matakan shari’a ba. Ya na da muhimmanci hukumar zaɓen ta ƙara faiyacewa masu zaɓe yadda na’urar ta BVAS za ta yi aiki da kuma yadda za a sakankance cewa za ta taimaka wajen hana duk wani yunƙuri na murɗiya.
An baiyana cewa na’urar za ta tattara dukkan bayanai ta yadda ko wani ya yi yunƙurin sauya alƙaluma to zai zama aikin baban giwa ya ke yi.
A zaɓen shekara ta 2011 tsohon shugaban hukumar zaɓen Farfesa Attahiru Jega ya kawo bayanin wata na’ura da a ka fassara da kamar randa ce a ofishin sa ta tara sakamakon zaɓe kai tsaye daga mazaɓa.
A zaɓen 2015 Farfesa Jega ya kawo na’urar tantance mai kaɗa ƙuri’a ta gane shi da tambarin yatsar hannun sa mai taken SMART CARD READER a turance.
Wannan na’ura ta yi aiki a wasu sassa inda a wasu kuma a ka samu jinlkirin kafin ta tantance. Wasu ma a gaskiya haka su ka haqura ba su kaɗa ƙuri’a ba don na’urar ba ta shaida su ba.
Koma dai me za a ce an samu wani babban sauyi a lokacin ta hanyar na’urar. A zaɓen 2019 ma da wannan na’urar a ka yi amfani wajen tantancewa. A zaɓen nan na 2023 mai zuwa hukumar zaɓen ta ce sabuwar na’urar ta BVAS cigaba ne kan na’urar SCR don ita baya ga tantance mai kaɗa ƙuri’a har sakamako za ta tara da gane duk bayanan mutum kai tsaye don rufe kowace kafa ta murɗiya.
Masu dari-dari da lamarin na’urar na kafa hujja da cewa a wasu sassa ba sadarwar yanar gizo don haka ba lalle na’urar ta yi aiki ba. Hukumar zaɓen wacce ta gwada amfani da na’urar a zaɓen gwamna na wasu jihohi ko ma a taƙaice a ce wata jiha ta ce ba gudu ba ja da baya da na’urar ta BVAS za ta gudanar da babban zaɓen.
Alamu na nuna ta ɓangaren hukumar zaɓe alƙalami ya bushe kan amfani da na’urar don haka sai masu kaɗa ƙuri’a su kwantar da hankali su fahimci yadda na’urar za ta yi aiki.
Hanyoyin magudin zaɓe a baya sun haɗa da amfani da yaran da shekarun su ba su kai zaɓe ba su shiga layi su yi zaɓen, dangwale ƙuri’u, satar akwatin zaɓe, sauya alƙaluman zaɓe a kan hanya da sauransu.
Duk bayanai sun nuna na’urar za ta hana duk waɗannan hanyoyin yiwuwa don za ta ma tura sakamakon kafin isowa da takardar tattara sakamako. Matuƙar dai za a samu ingantaccen zaɓe a Nijeriya da zai wakilci gaskiyar ƙuri’ar da masu zaɓe su ka kaɗa za a iya samun sauyin ɗabi’a daga ’yan siyasa don sun san lalle sai sun kyautatawa masu zaɓe kafin su isa tudun mun tsira.
Mutunta kai shi ne mai kaɗa ƙuri’a ya tafi rumfarsa a tsanake ya bi layi ya samu ya kaɗa ƙuri’arsa a asirce ba tare da neman tada hargowa ba. Wani babban ƙalubale game da zaɓen Nijeriya na 2023 shi ne siyasar kuɗi.
Ko daga zaɓukan fidda gwani an haƙiƙance an yi amfani da maƙudan kuɗi wajen sayen wakilai. Yadda a ka samu matuƙar ƙuncin tattalin arziki to a haƙiƙa ba za a kawar da yiwuwar wasu masu kaɗa ƙuri’a su karɓi kuɗin kwanon shinkafa su sayar da ƙuri’arsu ba.
Ai a baya da matsalar ba ta kai haka ba akwai masu rataya ganye a kunnen su a rumfar zaɓe don duk wanda ya biya su, sai kawai su kaɗa ma sa ƙuri’a. Dalilin su bai wuce cewa ’yan siyasa ba sa sake dawowa wajensu, sai lokacin neman ƙuri’a don haka gara su karɓi rabonsu kawai a huta.
Wannan dai ba farar dabara ba ce don in har ɗan siyasa ya san kuɗinsa a lokaci ɗaya za su saka ya samu ƙuri’a shikenan sai ya tara kuɗi ya jira sai lokacin zaɓe.
Ya na da muhimmanci masu kaɗa ƙuri’a su dage su kawar da kwaɗayin lokaci ɗaya don cin riba mai tsawo ko dogon zango. A guje wa tsohuwar maganar nan da a kan ce wasu masu zaɓe tamkar kaji ne sai an watsa mu su tsaba sannan a kan samu haɗin kansu.
Kuma a gaskiya wannan magana daga kudu ne ta kan taso tamkar zolaya ga ’yan arewa. Kishin zuci ya na da muhimmanci a nan wajen sauya duk wasu ɗabi’u mararsa riba a lamuran zaɓe don samun cin gajiyar mulkin dimokraɗiyya.
Matuƙar ɗan takara ya san sai ya cika alƙawarin kamfen kafin ya sake samun dama, to haƙiƙa zai dage wajen yin abun da ya dace kuma maganganun sa ba za su zama zaɓe a kan ruwa ba.
Wani abu kuma shi ne ko an tafi zaɓe ba tare da kwaɗayin komai ba, to lalle sai kuma an zaɓi wanda ya cancanta ko da ran mai zaɓen ba ya son ɗan takarar.
Abun nufi a nan shi ne mai zaɓe ya zaɓi wanda zai zama alheri ga kasa ko jiha da duk matakan zaɓe. A ƙasashen da su ka yi nisa a tsarin dimokraɗiyya da zaɓe, mutane kan iya barin ɗan takarar jam’iyyarsu matuƙar bai cancanta ba, su zaɓi ɗan takarar wata jam’iyya wanda ya cancanta.
Shi ya sa a ke yi wa ƙuri’a kirari da “ƙuri’arka ’yancinka” don mutum na da hurumin zaɓan duk wanda ya ga ya dace ba tare da wani ya tilasta shi ba.
Shugabar kwamitin zaɓe ta majalisar wakilan Nijeriya Aishatu Jibril Dukku ta jaddada cewa an tsara zaɓen 2023 ta hanyar da a ka toshe duk wata kafa ta maguɗi.
Aishatu Dukku na magana ne a taron wayar da kai ga masu yada labaru na yanar gizo na mazaɓarta kan nagartattun hanyoyin yaɗa labaru don gudanar da zaɓen bisa doka da oda.
Aisha Dukku ta ce ko da wani ya yi karambanin rugawa da akwatin zaɓe don wargaza sakamako na aikin baban-giwa ne don na’ura kai tsaye na ɗauka da ƙidaya ƙuri’un da a ka kaɗa.
Kazalika ta ce sabuwar na’urar na da tsarin gane mutum ta hanyar hoton sa ko da kuwa yatsun sa sun suɗe saboda noma ko wani aikin ƙwadago.
’Yar majalisar ta buƙaci ’yan Nijeriya su fito su kaɗa ƙuri’arsu ga duk wanda su ke so ba tare da shakkar rashin adalci ba.
Yayin da ta ke gargaɗin masu yayata labarun na yanar gizo da gujewa yada labarun karya ko na cin zarafin wani ɗan takara, Dukku ta ce doka ta tanada ɗaurin wata 6 ko biyan tarar Naira dubu 100 ga duk wanda ya yi karan-tsaye ga yaɗa labarun zaɓe.
Masanin kimiyyar siyasa na jami’ar Abuja Dakta Aabubakar Umar Kari ya duba irin labarun da ba a iya kauce mu su a kafafen labarun na yanar gizo da kuma ke da tasiri a zaɓen. Dr.Kari ya ce labarun sun haɗa da ɓangaranci, ƙabilanci da bambancin addini.
A nan Dr. Kari ya shawarci masu zaɓe su duba abubuwan da ’yan takarar su ka yi a baya don ganin wanda za su kaɗawa ƙuri’a. Hukumar zaɓe ta bayyana cewa kafafen yaɗa labarun yanar gizo musamman masu yaɗa jita-jita na kawo babbar barazana ga shirin zaɓen.
INEC ta ce sai an bi duk matakan tantancewa ne na tabbatar da kasancewar mutum ɗan ƙasa kafin yi ma sa rejista. Hukumar kai tsaye ba ta yi magana kan kama wasu da a ka yi kwanannan ’yan ƙasashen waje a Ibadan da rejistar zaɓe ba, amma ta ce a ɓangaren ta, sai ta tantance ne ta kan yi wa mutum rajista.
Hukumar zaɓen wacce ta kammala zagaye na ƙarshe na sabunta rejistar gabanin babban zaɓen 2023, ta baiyana filla-filla irin matakan da ta kan bi gabanin yin rajistar.
Jami’a a sashen labarun hukumar Zainab Aminu ta bayyana cewa har sai mutum ya zo da kofin shaida da za a gani ta zama ɗan ƙasa kafin samun damar.
Kammalawa;
Shugaba Buhari dai da zai kammala mulki bayan babban zaɓen ya tabbatar da wanda ya lashe zaɓe zai miƙawa ragama.
Masanin harkokin siyasa a Abuja Dr.Farouk BB Farouk ya aza shugaban a kan faifai da hasashen cewa ba zai tallafawa kowane ɓangare ba a siyasance.
Yayin da APC ke fatan zarcewa kan mulki jam’iyyun adawa na gwagwarmayar amshe madafu daga kammala wa’adin shugaba Buhari.
In za a tuna daga dawowa dimokraɗiyyar a 1999, PDP da ke zaman babbar jam’iyyar adawa yanzu ta yi mulkin tsawon shekaru 16 inda a 2015 gamayyar jam’iyyun adawa da su ka dunƙule ƙarƙashin shugaba Buhari su ka amshe ragama.
Za a jira a ga wanda zai kai labari a babban zaɓen da hasashe ke nuna komai ka iya faruwa kuma kai tsaye ba za a iya cewa ga lalle mai tagomashin lashe zaɓen ba.
