Daga SANI AHMAD GIWA
Ɗaya daga cikin ‘yan matan Kwalejin Tarayya da ke Birnin Yawuri a Jihar Kebbi da ‘yan bindiga suka sace ta haifi yaro namiji a sansanin da ‘yan bindigar ke tsare da su kamar yadda jaridar PRNigeria ta ruwaito.
Ɗalibar mai shekaru 16 wacce har yanzu ba a bayyana sunanta ba, ta kwashe sama da shekara ɗaya a hannun ‘yan bindigan da suka sace su a watan Yunin 2021.
Iyayen ‘yan matan dai sun koka kan yadda ‘yan bindigan suka kalmashe kuɗin fansa tare da aurar da ‘ya’yansu bayan garkuwa da suka yi da su.
Idan za a iya tunawa dai a watan Yunin 2021 ne ‘yan bindigar suka kutsa makarantar a babura inda suka buɗe wa ‘yan sanda wuta tare da raunata wasu ɗaliban yayin da mutum ɗaya ya rasa ransa.
Bayan kwanaki uku, a zagayen da sojoji suka yi, sun ceto uku daga cikin ɗaliban yayin da aka sake ceto wasu biyu a watan Agustan 2021.
A watan Oktoban 2021, gwamnatin Jihar Kebbi ta ce ɗalibai 27 da malamai uku da ‘yan bindigan suka sace sun shaƙi iskar ‘yanci.
“A yayin da gwamnati ballantana Atiku Bagudu, Gwamnan jihar Kebbi ya soke cinikayya da ‘yan bindigan waɗanda suka buƙaci kuɗin fansa, iyayen ɗaliban da aka sace sun haɗa kuɗi tare da biyan na fansa domin sako ‘ya’yansu,” wata majiya ta ce.
“Abin takaici ne yadda ‘yan bindigan suka karɓa maƙuden dukiya na fansa kuma suka aurar da waɗanda suka sace tare da ƙin sakinsu,” inji majiyar.
