Cutar shan-inna: Zamfara za ta yi wa yara 667,623 riga-kafi

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau

A matsayin wani mataki na ci gaba da bai ƙananan yara kariya daga cutar shan-ina, gwamnatin Jihar Zamfara ta ce za ta yi wa yara aƙalla 667,623 ‘yan ƙasa da shekara ɗaya da kuma shekara biyar allurar riga-kafin cutar.

Shirin ba yin allurar in ji gwamnatin, zai gudana ne a tsakanin wasu ƙananan hukumomi guda bakwai.

Ta kuma bayyana cewa, 125,964 daga cikin jimillar yaran
‘yan shekara ɗaya ne, sannan 542,669 ‘yan shekara biyar su za a yi wa riga-kafin.

Daraktan kula da riga-kafin cututtuka na hukumar lafiya a matakin farko na jihar Zamfara, Malam Lawali Bello ne ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da jawabi a wani taron tattaunawa da manema labarai da aka gudanar a hukumar.

Bello ya bayyana ya ce, hukumar UNICEF tare da haɗin gwiwar Hukumar Bunƙasa Kiwon Lafiya a matakin farko ta jihar ne suka ɗauki nauyin riga-kafin.

Ya yi nuni da cewa, ƙananan hukumomi bakwai da aka zaɓa don cin gajiyar shirin sun haɗa da: Maru, Anka, Talata Mafara, Birnin Magaji, Ƙaura Namoda, Bakura da kuma Bukkuyum.

Ya kuma ambaci matsalar rashin tsaro sakamakon ayyukan ‘yan bindiga a ƙananan hukumomin Maru da Bukkuyum, a matsayin ƙalubale wajen kaiwa ga wasu alummomin yankunan a lokacin gudanar da riga-kafin.

Gwamnati ta kuma ba da shawarar cewa ya kamata tawagar jiha ta samar da tsarin da za a bi domin shugabannin ƙananan hukumomi su sanya hannu cikin shirin a yankunansu a faɗin jihar don samun nasara.

Kazalika, Gwamnatin jihar ta umarci ƙungiyoyi da su wayar da kan jama’a a jihar kan muhimmancin riga-kafin cutar shan-inna ga ‘ya’yansu domin su samu lafiya.

By Editor