Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya sanya hannu a kan dokar inganta rayuwar masu buƙata ta musamman, wadda majalisar dokokin jihar ta zartar kwanan nan.
Gwamnan ya ce dokar za ta taimaka wajen sanya masu larurar nakasa a cikin tsare-tsaren gwamnati da suka shafi cigaban ƙasa.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya ce wanzuwar wannan doka ta inganta rayuwar masu larurar nakasa za ta ba da damar fito da wannan ɓangare na al’umma da nau’o’in buƙatunsu ta yadda za a shigar da su a cikin tsarin gwamnati, tare da share musu hawaye.
Dokar ta hana yi musu kallon ƙasƙanci, sannan ta yi tsari na sauƙaƙa musu rayuwa wajen shige da fice a gine-gine da ma’aikatun gwamnati, ga kuma tanadin da za ta na kaso na musamman na guraben aiki domin masu larurar nakasar.
Malam Yerima Sulaiman Ibrahim na cikin shugabannin masu buqata ta musamman ɗin a Nijeriya, kuma ɗaya daga cikin jagororinsu a jihar Kano, wanda ya ce suna murmushi har kunne, sakamakon sanya hannu da gwamnan ya yi a kan wannan doka.
Sai dai ganin cewa gwamnan ya rattava hannu a kan wannan dokar ne a wata gaba da wa’adin mulkinsa ke ƙarewa.
Wannan ne ya sa Malam Yerima Sulaiman ya ce mutanensa na so gwamnan ya yi wani abu kasa da zai sa hukumar kula da masu larurar nakasar ta ɗore har bayan zamaninsa.
A makon jiya ne majalisar dokokin jihar Kano ta zartar da wannan doka ta inganta rayuwar masu buqata ta musamman ɗin.
Sai ga shi a wannan makon Gwamna Ganduje bai tsaya wata-wata ba ya rattava mata hannu.
Waɗanda aka yi dokar domin su sun haɗa da masu larurar rashin gani, rashin ƙafa ko hannu, da larurar ji, da ta fata ko zabiya da larurar rashin yatsa wato kuturta da masu cutar laka da kuma galhanga.
