An rantsar da Ademola Adeleke a matsayin sabon Gwamnan Osun

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

An rantsar da Sanata Ademola Adeleke a matsayin sabon Gwamnan Jihar Osun a ranar Lahadi.

Da wannan, Adelek ya zama gwamna na shida aka zaɓa a jihar tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya ƙasar a 1999.

Alƙalin Alƙalan jihar, Mai Shari’a Oyebola Adepele-Ojo, shi ne ya jagoranci rantsar da Adeleke da misalin ƙarfe 11:45 na hantsi.

Bikin rantsarwar ya guda ne a babban filin wasannin motsa jiki da ke Osogbo, inda magoya bayan Jam’iyyar PDP da sauran baƙi daga ciki da wajen jihar suka haɗu don shaida rantsarwar.

A ranar 16 ga Yulin 2022 Adeleke ya lashe zaɓen gwamna da aka gudanar a jihar a ƙarƙashin Jam’iyyar PDP inda ya kayar da gwamna mai barin gado, Adegboyega Oyetola.

Ɗan takarar Shugaban Ƙasa na PDP, Atiku Abubakar, na daga cikin manyan baƙin da suka halarci bikin.

By Editor