Assalam alaikum. Bayan Babban Bankin Duniyan ya yi gargaɗin cewa, sabon kuɗin na iya yin illa ga harkokin tattalin arzikin talakawan ƙasar da ma ƙananan masana’antu saboda gajeren lokacin da bankin Nijeriya ya diba domin sauya tsofaffin kuɗaɗen zuwa sabbi.
Bankin Duniya wato World Bank mai Shelkwata a Washington DC ya bayyana gargaɗin a wani sabon rahoto ne da ya fitar a shafinsa na yanar gizo mai ɗauke da suna Nigeria Development Update a Turance.
Bankin Duniya ya nuna cewa sabuwar manufar za ta iya yin illa ga kanana ‘yan kasuwa musamman masu hada-hadar kuɗi na yau da kullum da kuma ƙananan masana’antu. Wani abu da kwararre a fannin tattalin arziki na ƙasa da ƙasa Shuaibu Idris Mikati ya ce gargaɗin da Bankin Duniya ya yi ba sabon abu bane.
Mikati ya ce, Bankin Duniya na bada irin wannan shawarwari ga ƙasashe ko masu tasowa ko ƙasahen Turai waɗanda suka riga suka cigaba.
Mikati ya ce wannan shawara ce aka bayar akan illoli da ka iya tasowa kan wannan sauyin launin wasu kuɗaɗe da Bankin Nijeriya ya yi.
Mikati ya ce wannan shawara ce da ya kamata a duba domin ana cewa ‘yan Nijeriya sun kai miliyan 220 amma in an duba waɗanda suke hulda da banki waɗanda suke da lambar ajiya wato BVN, ba su wuce miliyan 60 ba.
Saboda haka wannan ya nuna cewa masu ajiya a bankuna ba su da yawa sosai. Mikati ya ce abu ne da Bankin Nijeriya ya kamata ya duba saboda ya ɗauki mataki kaman yadda ya saurari koken mutane, wajen ƙara yawan kuɗin da za a cire a asusun bankuna.
Shi kuwa mai nazari a fanin tattalin arziki Yusha’u Aliyu ya yi tsokaci cewa tsarin yana da kyau amma ya kamata a fara shi daga manyan birane
Yasha’u ya ce, Babban Banki yana da dama da zai gudanar da wannan tsari amma ya kamata ya yi la’akari da irin mutanen da ya kamata su yi amfani da tsarin musayar kuɗi ta dandalin yanar gizo waɗanda yawancin su suna qauyuka ne kuma ba sa jin turanci balle su iya amfani da dandalin yanar gizo wajen mu’amala da kuɗi.
Yusha’u ya ce, Babban Bankin Nijeriya ya duba yadda zai yi gyara a wannan fannin domin ya ƙara yawan lokaci da za a iya musayar tsofaffin kuɗaɗen zuwa sababbin kuɗaɗe idan ba haka ba zai kawo ruɗani a harkar farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar baki ɗaya.
Akan haka ne gagarabadan Majalisar Wakilai Mohammed Tahir Monguno ya sha alwashin tada maganar karin lokaci da ma ta wayar da kan al’umma musamman na Jihohin Borno da Yobe idan majalisa ta dawo daga hutun ƙarshen shekara. Monguno ya ce yawancin ƙauyuka ba su da bankuna, kuma mutane dayawan gaske ba su da ilimin amfani da wayoyin su wajen mu’amalar kuɗi, gashi kuma ba kullum ake samun hanyoyin sadarwa ba.
Munguno ya ce, zai dage har sai ya ga an samu sauyi a lokaci na yin chanjin kuɗaɗen.
Abin jira a gani shi ne irin matakin da Babban Bankin Nijeriya zai dauka ganin cewa Bankin Duniya da ma yawancin ‘yan ƙasa sun nemi a ƙara tsawon lokaci saboda a samu a sauya tsofaffin kuɗaɗen ba tare da an musguna wa kowa ba.
Wasiƙa daga AHMAD MUSA, 07041094323.
