Daga BASHIR ISAH
An gano gawar wani yaro mai suna Oreoluwa Fatiniye ranar Talata a wani rafin Jihar Ogun.
Rahotanni daga jihar sun ce, wasu masunta ne suka gano gawar a rafin da ke yankin Adigbe-Obada a jihar.
Jaridar Premium Times ta ce, wannan na zuwa ne kwana uku da kashe iyayen yaron a ranar Sabuwar Shekara, wato Lahadin ta gabata, a Abeokuta babban birnin jihar.
An yi wa Kehinde Fatinoye da matarsa, Bukunola, kisan gilla ne a gidansu da ke GRA ta hanyar banka wa gidan wuta wanda har yanzu ba a gano ko su wane ne suka aikata ɗanyen aikin ba.
An ce yayin harin ne maharan suka sace Oreoluwa da wani kukun gidan.
‘Yan sandan yankin sun ce suna kan bincike kafin daga bisani su sanar da sakamakon binciken nasu.
