Tarihin Masarautar Dutse

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A wannan mako Blueprint Manhaja ta taɓo kaɗan daga cikin tarihin fitaccen Masarautar Dutse da ke Jihar Jigawa. Garin Dutse wanda a baya ake fi sani da Dutse Gadawur shi ne sabon sunan garin Garu wanda ya samu a cikin ƙarni na 13 sakamakon zuwan wani maharbi Babarbare mai suna Duna Magu. Tun kafin bayyanar wannan maharbi a wurin, akwai mutane da ke zaune a wannan yanki na Garu da ya koma Dutse daga baya:

Wannan gari na Garu, shi ne matsungunin fadar Masarautar Dutse. Tun kusan ƙarni na ɗaya ake kyautata zaton mutane sun zauna a wannan wuri da ke da duwatsun da suka dace da farauta da kuma muhallin zama.

Bayan wani lokaci an samu canje-canje inda wannan gari na Dutse ya tashi daga masarauta ya koma gunduma a ƙarƙashin Masarautar Kano, kuma daga baya a 1993 ya sake komawa masarauta kamar yadda yake tun farko.

Manufar wannan rubutu ita ce, ya zama wata kafa ta samun bayanai dangane da wannan masarauta mai daɗaɗɗen tarihi.

Asali:

Akwai maganganu dangane da fadar Masarautar Dutse. A wata faɗar an ce duwatsun da suka kewaye garin Garu suna alamta samuwar jama’a a wannan wuri tun lokacin da ɗan Adam yake amfani da dutse a matsayin hanyar samar da kayan amfani, lokacin da a Turance ake kira ‘Stone Age.’ (Sanusi, 2009).

A wata ruwayar kuma an ce akwai samuwar wani gari da ake kira Birnin Gija wanda ya tava zama cibiyar kasuwanci a yankin sahara (Trans-Saharan Trade) tun kafin samuwar birnin Kano. Shi wannan gari, ba ya da nisa da ainihin garin Garu a yanzu haka. Haka nan a wannan gari na Birnin Gija akwai sauran alamomin wuraren da aka gudanar da sana’ar rini. (Sanusi, 2009).

Sannan akwai waɗanda suka fara rubuta tarihin Dutse daga ƙarni na 13 lokacin da wani maharbi mutumin Borno mai suna Duna Magu ya bayyana a yankin. Wannan mutum shi ne wanda ya fara kiran wannan wuri da sunan Gadawur. (Sanusi, 2009). Daga baya kuma aka koma ana kiran wurin da Dutse Gadawur. Duna Magu mutum ne maharbi wanda a ƙoƙarinsa na gano wuri mafi dacewa da zai gudanar da sana’arsa ta harbi ya zo wannan yanki na Dutse, ya kuma yi sa’a wannan yanki wuri ne mai yawan gada. Da isarsa kan wannan dutse tun kafin ya gama sauke kayansa na harbi, sai ya hangi wata gada tana gudu, kafin ya waiga ya waigo sai gadar nan ta wulka kamar walƙiya ya neme ta ya rasa. Cikin mamaki sai ya kada baki ya ce, ‘yanzu na ga gada, wur ta wuce’ To, an ce tun daga wannan lokaci wannan suna na Dutse Gadawur ya zauna. (Masarautar Dutse, 2015; Ƙwalli, 1996; Sanusi, 2009).

Wannan shi ne asalin dutsen da Duna Magu ya sauka a kai, har yau wannan dutse yana nan a bayan fadar Masarautar Dutse a garin Garu. Sararsa da jama’a ke yi shi ya maida shi karami kamar yadda yake a hoton da ake gani.

Dangane da jimawa ko samuwar zaman jama’a a wannan yanki na Dutse kuwa, Masarautar Dutse (2015), ta ruwaito cewa, mutane sun zauna a wannan yanki na Dutse tun kafin Bagauda ya zo Kano. Sannan bayan Bayajidda ba da daɗewa ba an samu dangantaka ta yaqi a tsakanin wannan masarauta ta Dutse da Masarautar Kano kamar yadda ya zo a Northern Nigerian Publishers (1979). Haka akwai batun cewa kundin tarihin nan na Kano mai suna ‘Kano Chronicle’ ya bayyana cewa ɗaya daga cikin sarakunan Kano mai suna Abdullahi Barja (1438 – 1452), ya yaƙi Masarautar Dutse a zamanin Sarki Tuwai Mai Asarki Babba (1421 – 1463), wanda bayan ya yi galaba ya auri ’yar Sarkin Dutse da kuma ’yar Galadiman Dutse. (Northern Nigerian Publishers, 1979; Sanusi, 2009).

Dutse Gawur

Tun daga ƙarni na 13 zuwa yau (2016), wannan masarauta ta Dutse ta yi sarakuna 47 guda 28 kafin jihadi, 19 kuma bayan jihadin Shehu Ɗan Fodiyo. Sai dai cewa waɗansu daga cikin waɗannan shugabanni ba sarakai ba ne, a lokutan da Dutse ta riƙa zama a ƙarƙashin Kano a matsayin garin hakimi, saboda haka waɗansunsu hakimai ne ke nan, wadansu kuma sarakuna.

Masarautar Dutse na daga cikin masarautu masu daɗaɗɗen tarihi. Sai dai, ta samu tasgaro a wasu lokuta a baya, musamman zamanin da Sarkin Kano Abdullahi Barja ya yaƙe ta ta koma ƙarƙashinsa. Saboda waɗannan dalilai da wasu, sai ya zamo waɗansu sarakunan na Dutse a wasu lokuta a baya suna a matsayin hakimai ne ƙarƙashin Masarautar Kano.

Wannan masarauta ta Dutse, tana da gidajen sarauta guda uku kamar haka: Barebari (Kanuri), Haɓe (Hausawa), da kuma Fulani (Fulata-Borno).

Daga wancan lokaci zuwa yau (2016), wannan masarauta ta samu sarakuna 47. Na farkonsu shi ne Sarki Tuwai Mai Asarki Babba, na ƙarshe kuma zuwa yanzu (2016), shi ne Mai martaba Sarki Nuhu Muhammadu Sanusi.