Daga AMINA YUSUF ALI
Masu tafiyar da harkar sufurin jiragen sama a Nijeriya suna fuskantar barazanar ɗaurin shekaru biyu a kurkuku ko zaɓin biyan tarar Naira miliyan biyar ko dukkan biyun a sakamakon qin biyan haƙƙin gwamnati da ta sanya dokar kamfanonin su dinga biyan kaso 5% na kowanne kuɗin tikiti da aka saya na jirgi ko kuma idan aka biya kuɗin jirgin ɗaukar kaya da sauran kwangiloli.
Hukumar kula da harkar sufurin jirgin sama ta Nijeriya (NCAA) ita ta bayyana haka a ranar Talatar Makon da ya gabata. Inda ta gabatar da wannan sabuwar doka da take son tabbatarwa ta harkar sufurin Nijeriya (CAA) 2022 ga manema labarai.
Wannan jawabi dai ya zo ne bayan hukumar ta tuhumi kamfanonin sufurin jiragen sama na gida Nijeriya da yin hawan ƙawara a kan dokokin ƙasar da suka shafi kuɗi.
Hukumar ta NCAA ta yi ikirarin cewa, ko a cikin watan Agustan shekarar bara kamfanonin jiragen saman sun riƙe wa hukumar Naira biliyan 19 na harajin cinikin tikitin shiga jirgi. Wannan lissafi ya saɓa da Naira biliyan 37 da ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika ya faɗa a shekarar da ta gabata ya ce hukumar tana bin kamfanonin.
Sakamakon binciken da kafofin yaɗa labarai suka yi, ya gano cewa, kuɗaɗen harajin kaso biyar da za a samu daga cinikin tikitin jirgin gwamnati za ta raba shi ne a tsakanin hukumar Sufurin jiragen saman Nijeriya (NCAA), da hukumar kula da sararin samaniya (NAMA), Hukumar bincikar zaman lafiya (NSIB), da kuma hukumar kula da annoba ta Nijeriya (NiMET).
Sabuwar dokar dai ta bayyana cewa, dole a fitar wa da gwamnatin tarayya kaso 5 daga cikin dukkan kuɗaɗen da kamfanonin sufurin jiragen sama suka samu ta hanyar sayar da tikiti ko a ƙasar nan ko ma a wasu ƙasashen, ko wata kwangila, ko biyan kuɗin wani aiki da sauransu. Dukkan hukuma tana da kaso 5 na wannan kuɗin.
Dokar ta ƙara da cewa: “duk wani kamfanin da ya yi buris da wannan doka ta biyan kaso biyar a cikin ɗarin, ya aikata babban laifi kuma daraktocinsa za su biya tarar Naira miliyan biyar, ko su fuskanci zaman gidan yari na shekara 2 ko kuma dukka biyun”.
