Wa’adin tallafin mai: Nijeriya za ta kashe tiriliyan N3 kafin Yunin 2023

Daga BASHIR ISAH

Ministar Kuɗi, Zainab Ahmed, ta faɗa ranar Laraba cewa Nijeriya za ta ci gaba da ba da tallafin fetur har zuwa tsakiyar 2023, kuma ta ware kuɗi N3.36 da za ta kashe kan tallafin.

Majiyarmu ta ce tsakanin Janairu zuwa Satumba na 2022, ƙasar ta kashe tiriliyan N2.91 wajen ba da tallafin fetur, lamarin da gwamnati ta ce ya haifar da gibi a asusunta.

A Talatar da ta gabata Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaɓa hannu kan kasafin 2023 na tiriliyan N21.83 bayan ‘yan majalisa sun yi ƙarin kashi 6.4 cikin 100 kana suka ɗaga hasashen farashin mai.

A cewar Ministar, “Za a ci gaba da ba da tallafin fetur zuwa tsakiyar 2023 bisa la’akari da ƙarin wata 18 da aka yi kamar yadda aka sanar a farkon 2022.”

A watan Oktoban da ya gabata aka jiyo Buhari ya ce ƙasar za ta dakatar da bayar da tallafin mai a 2023, inda zai sauka ya bai wa sabon shugaba ragamar mulki a Fabrairu.

Gwamnatocin da suka gabata sun yi yunƙurin cire tallafin mai ɗin baki ɗaya amma hakan ya faskara.