Ni ɗan wasa ne na musamman, inji Ronaldo

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Cristiano Ronaldo ya bayyana kansa a matsayin ɗan wasa na musamman, sannan ya haƙiƙance cewa, zamaninsa bai ƙare ba a daidai lokacin da ya koma sabuwar ƙungiyarsa ta Al Nassr da ke ƙasar Saudiyya.

Ɗan wasan gaban na Portugal mai shekaru 37, ya rattaba hannu kan gagarumar yarjejeniyar da aka kiyasta darajarta kan Yuro miliyan 200 bayan ya kammala zamansa a Manchester United da Real Madrid da Juventus.

“Ni ɗan wasa ne na musamman. Na ji daɗin zuwa nan, na kafa dukkanin tarihi a nahiyar Turai, kuma ina son na kafa a Saudiyya,” inji Ronaldo.

Ɗan wasan ya kuma ƙara da cewa, maƙasudin zuwansa Saudiyya shi ne samun nasara, walwala, da kuma bada gudunmawa ga fannin ci gaban ƙasar da raya al’adunta.

Ronaldo ya ce, ya yi ban-kwana da nahiyar Turai, yayin da ya yi watsi da tayin da aka yi masa a Turai da Brazil da Australia da Amurka har ma da Portugal a cewarsa.

A ɗaya ɓangaren kuma, Kocin Newcastle Eddie Howe ya ce babu ƙamshin gaskiya a rahoton da ke cewa akwai wani sashi cikin yarjejeniyar Cristiano Ronaldo da Al Nassr, da ke cewa yana da damar tafiya ƙungiyar Newcastle United a matsayin aro, idan ta samu gurbin shiga gasar zakarun Turai.

A ranar Talata ƙungiyar Al Nassr ta gabatar da Ronaldo gaban magoya bayanta, bayan da suka ƙulla yarjejeniyar kimanin Yuro miliyan 200 a tsawon shekaru biyu, wato daga yanzu har zuwa watan Yunin shekarar 2025.

Ɗan wasan mai shekaru 37 ya rabu da Manchester United ne a watan Nuwamba, bayan da ya yi wata hira inda ya soki kocinsa Erik ten Hag da shugabannin ƙungiyar.

Sai dai wani rahoto da aka buga a ƙasar Spain cikin wannan makon ya bayyana cewar ɗan wasan da ya lashe kyautar Ballon d’Or sau biyar ya fara tunanin yiwuwar komawa gasar Premier.

Rahoton ya ce a cikin yarjejeniyar da ya sa wa hannu, Ronaldo da damar bugawa Newcastle, wadda kashi 80 na hannun jarinta mallakin ‘yan ƙasar Saudiyya ne.

To amma kocin ƙungiyar ta Newccatle Eddie Howe ya shaida wa Sky Sports cewa suna yi wa Cristiano fatan alheri a sha’aninsa, sai dai babu ƙamshin gaskiya a cikin rahoton zai buga musu wasa a matsayin aro.