Ba mu da ikon hana mahandama sake mallakar kadarorinsu da EFCC ta yi gwanjonsu – Majalisar Wakilai

Daga AMINA YUSUF ALI

Kwamitin Majalisar Wakilai na Musamman kan tantance kadarorin da aka sata na gwamnati masu motsawa da girkakku tun daga shekarar 2000 zuwa 2022 sun bayyana cewa, ba su da ikon hana barayin gwamnati daga sake mallakar kadarorinsu da gwamnati ta ƙwace ba, a wannan gwanjo da ake yi na dukkan kadarorin da gwamnati ta ƙwace daga jami’an gwamnati da suka yi sama-da-faɗi da su. 

Shugaban kwamitin gaggawa na ‘yan majalisar na gwanjon kayan gwamnati Honarabul Adejoro Adeogun ya bayyana cewa, da ma tuntuni kwamitin da yake jagoranta ya faɗa wa hukumar yaƙi da cin Hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC), ta tsara wasu hanyoyi waɗanda za su hana barayin gwamnati sake samun damar mallakar kayan da suka sata a wannan gwanjon  da ake kan yi.  

A cewar sa, abu ne mai sauƙi ga barayin gwamnati su yi kurɗa-kurɗa don sake mallakar kayansu da aka ƙwace, kuma a cewar sa, majalisar ba ta da iko a kan yanke hukunci a kan yadda za a ba wa ko sayar wa da kadarorin.

Ya ƙara da cewa, da ma gudun wannan ne ya sa majalisar tuntuni ta buƙaci EFCC ta dinga yin gwanjon kowacce kadara da zarar an ƙwace ta. A cewar sa, wannan yana daga abubuwan da suka rubuta a rahotansu na ƙorafi. Sannan kuma a cewar sa, wasu kadarorin ma an ƙwace su ne kusan shekaru 7 zuwa 8 da suka gabata, a yanzu darajarsu ta riga ta karye da kaso 80 zuwa 90 saboda rashin ajiya mai kyau. 

A cewar Honarabul Adeogun, faɗuwar darajar kayan ma abin damuwa ce, musamman a wannan lokacin da gwamnatin tarayya take neman kuɗi ido rufe don ciko a kasafin kuɗin ƙasar na bana. 

A cewar sa, majalisar ta yi iya ƙoƙarin da za ta yi, amma abin ya ci tura. Ba su samu haɗin kai daga hukumar yaƙi da ta’annatin ba. 

Idan za a iya tunawa dai tun a ranar 6 ga watan Disamban 2022, hukumar EFCC ta sanar da fara dubawa da yin gwanjon ababen hawan da ta ƙwace guda 649 waɗanda suke a faɗin jihohin Nijeriya dukkansu da kuma birnin tarayyar Abuja, waɗanda zaɓaɓɓun masu gwanjo za su gudanar. 

Sauran kadarorin da aka lissafa a cikin kayan da za a yi gwanjon sun haɗa da manyan jiragen ruwa guda 15 a jihar Ribas, Delta da kuma Legas; sai wayoyin hannu guda 39, da kwamfuta samfurin laftof guda 11, da sauran na’urori.  

Hakazalika, rahotanni sun bayyana cewa, akwai kuma manyan gidaje da filayen na alfarma guda 144 da hukumar ta EFCC ɗin ta ƙwata daga ‘yan siyasa da aka tuhuma da yin hainci da rashawa, har ma Ma’aikatan gwamnati da ‘yan kasuwa ɓata-gari, da mazambatan intanet, waɗanda aka tuhuma da laifuffukan rashawa, hainci, karkatar da kuɗaɗen gwamnati zuwa buƙatun ƙashin-kai, da kuma sama-da-faɗi da kuɗaɗen gwamnatin.