Daga RABIU SANUSI, Kano
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta yi nasarar damƙe Nura Auwal da abokinsa Abubakar Lawal bisa zargin garkuwa da wasu yara ƙanana.
Sanarwar da Rundunar ta fitar ta bakin mai magana da yawunta, SP Haruna Abdullahi Kiyawa, ta ce iyayen yaran da ke zaune a Unguwar Bachirawa cikin Ƙaramar Hukumar Ungoggo a jihar, sun kai rahoton ɓacewar ‘ya’yan nasu ofishin ‘yan sanda na yankin.
Ta ce masu garkuwar sun tura wa da iyayen rubutacciyar takarda ɗauke da lambar sunan asusun banki da lambar waya don tattauna kuɗin fansa Naira miliyan biyu da suka nema kan kowane yaro.
Rundunar ta ce da samun wannan rahoto, Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Mamman Dauda, ya umarci tawaga ƙarƙashin jagorancin SP Muhammad Aliyu Auwal mai kula da sashen masu laifin garkuwa da mutane na rundunar dan kuɓutar da yaran tare da kama waɗanda ke da alhakin aikata laifin.
Sanarwar ta ce cikin ƙwarewa tawagar ta duƙufa aiki inda a ƙarshe ta bankaɗo waɗanda ake zargi da sace yaran, kana an kuɓutar da su.
Rundunar ta ce waɗanda ake zargin sun amsa tuhuma.
Tare da ce za a gurfanar d waɗanda ake zargin a kotu da zarar jami’anta sun kammala bincike.
