Allah Ya yi wa Farfesa Ibrahim Umar rasuwa

Daga WAKILINMU

Allah ya yi wa tosohon mataimakin shugaban Jami’ar Bayero da ke Kano, Farfesa Ibrahim Umar rasuwa.

Majiya daga ahalin marigayin ce ta tabbatar da rasuwar ga jaridar Daily Nigeria, inda ta ce ya rasu ne ranar Litinin a Kano.

Marigayin wanda shi ne malami na farko da ya fara koyar da darasin ‘Physics’ a BUK a shekarar 1976, ya zama mataimakin shugaban jami’ar ne daga 1979 zuwa 1986.

Kazalika, ya riƙe Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Minna, babban birnin Jihar Neja.

A zamaninsa an samu cigaba mai ma’ana wajen yi wa BUK gine-gine da dama.

Da shi aka yi aikin shirya Kundin Tsarin Mulki a 1978 na Jamhuriya ta biyu, kuma ya wakilci Nijeriya a Babban Taron Makamashi na Duniya da ya gudana a 1990 da dai sauransu.