Da Ɗumi-ɗumi: Gobara a Kotun Ƙoli a Abuja

Spread the love

Bayani da ɗumi-ɗumi da muka samu da safiyar Litinin ya nuna cewa, gobara ta tashi a wani sashen ginin Kotun Ƙoli da ke Abuja.

Sai dai ya zuwa haɗa wannan labari ba a kai ga ayyana dalilin tashin gobarar ba.

Amma a hango wasu ma’aikata yayin da suke ta ƙoƙarin kawar da kayayyaki a wasu sassn ginin gudan kada gobarar ta shafe su.

Kazalika, an ga jami’an kwana-kwana sun ba da himma wajen kashe gobarar.

Wannan na zuwa ne kwana biyu bayan da ‘yan takarar shugabancin ƙasa na Jam’iyyun PDP da LP, wato Atiku Abubakar da Peter Obi, suka shigar da ƙara kotun bayan da suka sha kaye a kotun farko.

Su biyun na neman kotun da ta yi watsi da sakamakon babban zaɓen 2023 wanda Bola Tinubu na Jam’iyyar APC ya lashe.

By Editor