An naɗa Alhaji Adamu Ibrahim Wanki a matsayin sabon Daraktan Ma’aji na Hukumar Birnin Tarayya, Abuja.
Wanki ya zama sabon Daraktan ne biyo bayan ritayar da mai riƙe da muƙamin, Alhaji Zanna Hamza, ya yi a sakamakon cika shekara 60 da ya yi a bakin aiki.
Bikin miƙa ragamar ofishin ya gudana ne a babban zauren taron sashen tsarin tattalin arziƙi da ƙididdiga na FCTA da ke area 11, Abuja.
Taron ya samu halartar daraktoci na sassa daban-daban haɗi da sauran jami’an FCTA.
Kafin naɗin nasa, Alhaji Adamu Ibrahim Wanki shi ne jami’i mafi girma a sashen nasu.
Sashen ma’ajin FCTA shi ne sashen da ke kula da sha’anin kuɗi na hukumar wanda kulawar kuɗaɗen shiga na ciki da waje da akan tara ke ƙarƙashinsa.
