Kotun Sauraren Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen Gwamna a Jihar Legas, ta tabbatar da Gwamna Babajide Sanwo-Olu a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar.
Da yake karanto hukuncin a madadin sauran alƙalan yayin zaman kotun a ranar Litinin, Mai Shari’a Mikail Abdullahi ya ce ƙarar da Jam’iyyar PDP da ɗan takararta, Olajide Adediran, suka shigar ba ta da daraja wanda hakan ne ya sa kotu ta kori ƙarar.
Tuhumar da ake yi wa Gwamnan Sanwo-Olu ta haɗa da amfani da takardun bogi da kuma cewa jam’iyyarsu ta APC ba ta tsayar da shi da mataimakinsa takara bisa ƙa’ida ba.
Bayan sauraren duka ɓangarorin, a ƙarshe sai kotu ta yanke hukuncin cewa, “ƙarar ba ta daraja don haka kotu ta yi watsi da ita.
“Na tabbatar da Babajide Olusola Sanwo-Olu a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan Legas….” in ji kotun.
