Ambaliyar ruwa ta raba mutane 563 da muhallansu a Adamawa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ambaliyar ruwan sama ta raba mutane 563 da ke Unguwan Tana a Ƙaramar Hukumar Yola ta Gabas a jihar Adamawa.

Mutanen da iftila’in ya shafa, a yanzu haka sun samu mafaka a makarantar sakandare ta je ka ka dawo ta GDS da ke yankin Limawa-Jimeta, a Yola babban birnin jihar.

Shugaban makarantar Musa Hassan Jada ya bayyana cewa, mutanen da abin ya shafa sun tare a ajujuwa bakwai na makarantar.

Kazalika, mataimakin gwamnan jihar Kaletapwa George Farauta, ya ziyarci Unguwan Tana domin duba irin varnar da ambaliyar ruwan ta janyo.

Bugu da ƙari, George ya yi alƙawari gwamnatin jihar, za ta kawo masu ɗauki domin a rage masu raɗaɗin zafin aukuwar iftila’in na ambaliyar ruwan.

Amabilayar ruwan dai ta auku ne sanadiyyar cikar da kogin Benuwe ya yi biyo bayan yin ruwan sama kamar da bakin ƙwarya tare da kuma sako ruwan Dam na Lagdo da ke a jamhuriyar Kamaru.

By Editor