Shehun shehunan Larabci a Nijeriya, Ogunbiyi

Spread the love

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Na taɓa wani rubutu da daɗewa ina mai cewa duk Musulmin Nijeriya na jin harshen Larabci ko da kuwa basa iya magana kai tsaye da harshen. In mun duba yadda a kan ba da umurni da harshen ka ga sun yi abun da a ka faɗa za a iya amincewa cewa batun haka ya ke. Alaƙa da addini kasancewar da harshen a ke magana ya yi matuƙar taimakawa wajen fahimtar harshen.

A sallar Juma’a liman zai ce “ƙuumuu ila salaatikum…” sai ka ga manya da yara duk sun miƙe don fahimtar abun da a ka faɗa. Haka nan gaisuwa ma kusan kowa na iya yi da harshen don kasancewar sa harshen Manzon Allah mai tsira da aminci ga shi kuma shi ne harshen Alƙur’ani mai girma. Kai ko ta barkwanci ma irin masu cewa “shinkfa kaza ma’a shayi” na nuna fahimtar da mutane ke yi wa harsahen. Son samu duk wanda ya je qasar Larabawa daga nan Nijeriya ta Arewa ya iya fahimtar bayanai yanda ba zai ka sa hulɗa da jama’a ba.

Masu amfani da harshen Hausa ma musamman ya kamata a ce sun koyi Larabci ko da na sadarwa ne don akwai tarin kalmomi a yau na Larbaci a cikin harshen Hausa kuma sun zauna daram kamar dama Hausar ce. Zai yi wuyar gaske mutum ya yi magana ta tsawon daƙiƙa 10 bai sa harshen Larabci da Huasawa su ka ara ya koma cikin harshen su ba.

Koyon harshe ai babban jari ne a rayuwa don haka ya na da muhimmanci kowa ya koyi wani harshen waje da harshen sa na haihuwa. Zai zama babban abun takaici ya zama mutum ya kare rayuwar sa in ka jijjiga shi ka taras bai ƙware a harshen sa na asali ba balle a je ga batun wani daga manyan harsunan duniya. In ka shiga yanar gizo ka duba shafukan sadarwa na mutane za ka ga wasu na rubuta sun iya harshen su da turanci ko Larabci da sauran su.

In ka bincika sai ka taras ba lalle kowane mai irin wannan ikirarin ya gwanance a harsunan da ya rubuta ba. Gwanancewa na nuna sanin nahawu ko ƙa’idojin haɗa jumla a harshe da kuma wasu matakai na bambance jinsin maza da mata da iya furta kalmomi waɗanda a ke ja da waɗanda ba a ja.

Hakana nda iya fadar sunayen mutane yadda ma’abota harshe ke faɗa. Kazalika ko da mutum ya kware za ka iya samun wani baya lura da wasu kalmomin da sai ya ƙara koyar yadda a ke furta su a asalin harshen. Misali ga masu magana da harshen ingilishi sun san akwai bambanci wajen furta kalmar “P” da “F” kuma an fi samun waɗanda ba su kula da wannan bambancin a tsakanin Hausawa.

Su kuma Yarbawa na da tasgaron bambance “A” da “H” a harshen Ingilishi. Mutan Igbo na na tawayar bambance kalmar “R” da “L” kuma hakan kamar na da wuyar gyarawa in ba mutum shi kaɗai ya zauna ya lura akwai wannan ƙalubale ba da ya kan taso don yadda harshen asali kan yi tasiri a wajen furta kalmomin. Wata damuwar ita ce halin ko in kula ta yadda mutum kan furta kalma wai in za a iya fahimta ai shikenan irin abun da a ke cewa burin ma je haji sallah.

Hikimar koyon harshe kan fara daga gaisuwa da tambayar inda mutum zai je ga abubuwan da a ke yi na yau da kullum irin cin abinci, tafiya kasuwa, gona, ta’aziyya. ziyara. makaranta da sauran su. Kazalika ƙoƙarin magana da waɗanda su ka kware ba tare da jin shayi ba na da tasiri wajen gwanancewa.

Haƙiƙa an yi sa’a inda harshen Hausa na daga cikin harsunan duniya da a ke amfani da su a ƙasashe fiye da tushen harshen. Na samu labarin ba za a lissafa harsuna 10 na duniya ba tare da ambata harshen Hausa ba ko da zai zo a na 11 ne.

Nan dai ba kan Hausa na ke son yin rubutun ba amma yadda Hausawa za su fahimci yaya matsayin harshen Larabci ya ke a Nijeriya da mamakin yadda wanda ya samu shaidar ƙwarewa a harshen a Nijeriya ba Bahaushe ba ne kuma ba ma mutumin Arewa ba ne haka nan ba ma Musulmi ba ne.

Asusun koyar da harshen Larabci na Nijeriya ya yi alwashin amfani da gwanancewa a harshen wajen yaqi da aƙidar ta’addanci a Nijeriya da ƙasashen yankin Sahel. Ma’ana ƙasashen da ke yankin Sahara kamar Nijeriya, Nijar, Chadi, Kamaru da makwabtan su.

Masana daga jami’o’i sun gabatar da jawabai a gagarumin taron gasar waƙa da Larabci da a ka gudanar a Abuja bisa tallafin masarautar Shraja ta Daular Larabawa. Ƙwararru na harshen Larabcin sun taru a Abuja inda su ka yi ta zuba Larabci kamar ruwan sama kuma dukkan su daga arewacin Nijeriya su ke kuma ba Balarabe ko ɗaya a taron.

Tun shiga ta ɗakin taro a cibiyar bunƙasa rayuwar mata da ke tsakiyar Abuja na fahimci matukar mutum bai yi karatun Larabci aƙalla na IFTIDA’IYYA ba wato firamare to sai dai ya zama ɗan kallo ko in an yi tafi shi ma ya zama tamkar ɗan a bi Yarima a sha ƙida. Na shiga ta ƙofar baya don hakan ya ba ni damar karantar yawan mutanen da su ka zo ba tare da ɗaukar hankalin na babban teburi ba.

A layin gaba manyan farfesoshi ne kusan guda 3 su ke zaune inda gefen su kuma masana Larabaci ne da su ka zo don gabatar da waka a gasar. Mahalarta taron maza ne da mata. An gabatar da jawaban da Larabci inda a kan fassara da turancin ingilishi amma ba Hausa. Da alamun duk mahalarta na fahimtar abun da a ke fada don su kan yi tafi ko ka ji an ruxe da kalmomi irin “na’am…jayyid, ahsant..”

“Ai cikar adon musulmi na tabbata ne da ƙwarewa wajen iya magana da harshen Larabci kuma koyon harshen wata riba ce ta hulɗa da jama’a a sauran sassan duniya” Inji Farfesan Larabci na cibiyar Larabci ta Nijeriya da ke Ngla Ibrahim Muhammad.

Farfesa Muhammad ya ce mafi gwanancewa a harshen Larabci a Nijeriya mabiyin addinin Kirista ne da hakan ke nuna harshen na kowa ne “sunan sa Farfesa Ishaak Ogunbiyi wanda a kan kasa duk lamuran Larabci da shi a duniyar Larabawa.”

Ogunbiyi wanda ya yi ritaya a yanzu ya na zaune ne a London kuma a kan gaiyace shi ƙasashen Larabawa irin Saudiyya don dubawa da tabbatar da ingancin lamura na ilimi da a kan yi amfani da su a koyar da Larabci.

A nan Farfesa Ibrahim Muhammad ya ce wannan ya nuna harshen Larabci na kowa ne a duniya ba lalle sai Larabawa ko Musulmi ba. Za a iya gane haka don akwai Larabawa waɗanda Kirista ne a ƙasashe irin Lebanon, Jodan, Masar, yankin Palasdinawa da sauran su. Larabawa mabiya addinin Kirista na ibadar su da Larabci da amfani da littafin Linjila na tsohon alkawari da sabon alƙawari da a ka fassara da Larabci. Ko don a ƙara fahimta Attaura da Linjila da mabiya addinin Kirista ke amfani da su a zamnin yau.

Masanin Larabcin na yankar shakku ya shawarci duk ’yan Nijeriya su koyi harshen don zai samar mu su ribar rayuwa. Ya yi amfani da damar wajen yabawa gwamnatin Nijeriya don ƙarfafa cibiyar bunƙasa harshen Larabci ta ƙasa a Ngala.

Shugaban asusun Dr.Umar Adam Gusau ya ce ta hanyar ƙwarewa a harshen zai taimaka wajen fahimtar addini da zai kawar da gurguwar fassara da kan kawo masu kauce hanya da sunan addini. A mahangar Dr. Gusau masu tsaurin ra’ayi da sunan addinin Musulunci har ya kan kai su ga ta’addanci na yi wa kalmomin Larabci mummunar fassara ce don haka ba sa fahimtar addinin Musulunci kamar yadda ya ke a shari’an ce daga magabata.

Daga sashen Larabci na jami’ar Abuja Farfesa Ndagi Muhammad ya ce za a koyi harshen da sauqi in a ka fara koyar da shi daga gida. Ndagi ya ba da shawarar duk iyaye da ke son ’ya’yan su, su koyi harshen sosai su riƙa jefa mu su ’yan kalmomin daga gida. Babban malamin na jami’a ya ce wata babbar damuwa ga mutane a Nijeriya kan ɗauka in su ka koyi Larabci ba za su samu aikin yi mai tsoka ba fiye da fassara da ko ayyukan addini da ba romo a ciki.

Mawaƙa masu magana da Larabci kamar ruwa irin Dr.Ibrahim Mu’azzam sun gabatar da baituka kan lamuran rayuwa.

Harshen Larabci ya dade a arewacin Nijeriya don huldar kasuwanci tsakanin yankin da ƙasashen Larabawa na arewacin Afurka da kuma dalilin tafiya Makkah don aikin hajji.

Kammalawa;

Ya na da kyau duk mu farka wajen koyon aƙalla ɗaya daga manyan harsunan duniya da su ka haɗa da Larabci, Turancin ingilishi da Faransanci. Ko mutum bai haɗa da Sinanci, Rashanci ko Farisanci ba, zai iya zagawa yankunan duniya ya yi hulɗa da jama’a cikin girmamawa da nishaɗi. Hakanan ta fuskar ciniki da mu’amalar al’adu. Ƙalubale ne ma musamman ga wanda harshe ɗaya tak ya ke iya sadarwa da shi a rayuwar sa da zan iya zaiyana hakan da ragon azanci.

By Editor