Gwamnan Zamfara ya yi kira ga malamai kan riƙo da gaskiya

Spread the love

*Ya jaddada aniyarsa kan ƙaurace wa sulhu da ‘yan bindiga

A yau Juma’a, Gwamnan Dauda Lawal, ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ƙauracewa duk wani batun sulhu da ɓarayi a faɗin Jihar Zamfara.

Gwamnan Ya bayyana haka ne a yayin da ya halarci taron wa’azi na mako-mako da aka saba gudanarwa a Gusau, inda ya hori Malaman Addini da su kasance masu riƙo da gaskiya.

Wata takardar sanarwar manema labarai da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta ce wannan taron wa’azin mako an kwashe shekaru ana gudanar da shi, kuma wannan shi ne karo na 1, 179.

Ya ƙara da cewa, gwamnan ya yi kira ga dukkanin shugabannin ɓangarorin al’umma da su kasance masu gaskiya a dukkanin hulɗoɗinsu, tare kuma da yawaita addu’ar wanzuwar zaman lafiya a Jihar ta Zamfara.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Gwamna Dauda Lawal, a yayin da yake jawabi a wurin taron wa’azin mako a Gusau, ya bayyana irin hatsarin da yake tattare da yin sulhu da ‘yan bindiga, inda ya ce, babu abin da sulhun zai haifar sai ƙarin ƙarfi gare su, tare da ci gaba da jefa al’umma cikin hatsari.

“Ya bayyana cewa dole ne a fuskanci gaskiya, domin kuwa waɗannan lalatattun sun nuna cewa ba wai sulhun suke son yi da gaske ba, saboda sun kasance masu saɓa alƙawari. Babu abin da ya rage face a durfafe su da ƙarfin tsiya.

“Gwamna Lawal ya kuma yi kira ga shugabanni, sarakuna da malamai da su riƙa faɗin gaskiya komi ɗacinta, ba tare da la’akari da wa ta shafa ba, komi daɗi ko rashin daɗinta.

“Ya yi kira ga shugabannin siyasa da al’umma da su muhimmanta lamarin tsaron jihar gaba da siyasa, domin zaman lafiyan Zamfara shi ne gaba da komi.”

Tun farko dai, a nashi lakcar, shugaban Kwamitin Zakka da Waƙafi na Jihar Zamfara, Sheikh Ahmad Umar Kanoma, ya yi dogon jawabi a kan muhimmanci sulhu, inda ya kawo sharuɗɗan da addinin musulunci ya gindaya wurin yin sulhu, da kuma yanayin da bai yiwuwa a yi sulhu a addinance.

By Editor