Tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida, Bello Maitama Yusuf, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekara 76.
Wani na kusa da marigayin, Hussaini Dalhatu, shi ne ya tabbatar da rasuwar nasa a ranar Juma’a.
Ya ce za a yi jana’izar Sardauna Dutse a fadar Sarkin Kano bayan an sauko daga Juma’a.
A halin rayuwarsa, marigayin ya yi sanata daga shekarar 1999 zuwa 2007.
Kuma ya riƙe muƙamin Ministan Harkokin Cikin Gida a 1981, sannan Ministan Kasuwanci 1982.
An haifi Bello Maitama Yusuf ne garin Gwaram, Jihar Jigawa a shekarar 1947.
